Isra’ila ta mayar da wani asibiti barikin soji a Gaza

 Isra’ila ta mayar da wani asibiti barikin soji a Gaza



Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun mayar da asibitin Al-Awda barikin sojoji.


Ma’aikatar ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar inda ta ce a halin yanzu sojojin na Isra’ila na rike da Falasdinawa 240 a cikin asibitin wadanda suka hada da marasa lafiya da ma’aikatan asibitin da wadanda suka rasa muhallansu.


Isra'ila ta kashe Falasdinawa 25 a birnin Rafah



Isra’ila ta kashe Falasdinawa 25 a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya bayyana.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da kai hare-hare a cikin gidaje da asibitoci a Gaza.


Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe mutum 19,453 a Zirin Gaza wadanda akasarinsu yara ne da mata.

Post a Comment

0 Comments