Isra'ila tana hana aiwatar da shirin MDD na kai kayan agaji Gaza —Falasdinu.

 Isra'ila tana hana aiwatar da shirin MDD na kai kayan agaji Gaza —Falasdinu.




Falasdinawa sun zargi gwamnatin Isra'ila da yunkurin hana aiwatar da kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2720 da ya bukaci a kai kayan agaji Gaza.


Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Falasdinu ta fitar ta ce Isra'ila ta mayar da yankin Gaza zuwa "wata babbar makabarta ta fararen-hula."


Ta yi tir da hare-haren da Isra'ila take zafafa kaiwa yankin da kuma kisan kare-dangin da take yi wa Falasdinawa da "kakkausar murya".


Sanarwar ta ce Isra'ila ta matsa kaimi wurin yin luguden wuta a yankin abin da ke nuna "bijirewar da take yi wa al'ummar duniya," lamarin da ya sa “Isra'ila ta zafafa kai hare-hare a kowanne yanki daga arewaci zuwa kudancin Gaza, inda take rusa dukkan wuraren zama da kuma kai hari kan dukkan 'yan'adam a arewacin Gaza” matakin da ya kara fito da zaluncinta.


Hakan ya nuna cewa tsare-tsaren Isra'ila sun mayar da hankali wurin yunkurin hana aiwatar da kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.


 Ministocin Wajen Turkiyya da UAE sun tattauna kan halin da ake ciki a Gaza


Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki a Gaza, a cewar wasu majiyoyin diflomasiyya na Turkiyya ranar Asabar.


Fidan da Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan sun tattauna kan kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya game da halin da ake ciki a Gaza da kuma kai kayan agaji.


Fidan ya bayyana muhimmancin yin amfani da wannan dama wajen kai kayan agaji da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar bai wa Falasdinu kasa mai cin gashin kanta.

Post a Comment

0 Comments