Isra'ila tana yin 'wasa' da rayukan 'yan kasarta da aka yi garkuwa da su don ba ta son daukar nauyi: Qassam

 Isra'ila tana yin 'wasa' da rayukan 'yan kasarta da aka yi garkuwa da su don ba ta son daukar nauyi: Qassam



Mai magana da yawun Qassam Brigades ya ce da gangan Isra'ila ta kashe uku daga cikin sojojinta.

Reshen soji na kungiyar Hamas wato Qassam Brigades ya ce Isra'ila tana wasa da rayukan sojojinta da aka yi garkuwa da su, shi ya sa ma ranar Juma'a ta kashe uku daga cikinsu da gangan.


Ya ce yana cikin shirin Isra'ila na kin daukar nauyin da ya rataya a wuyanta.


Kakakin Qassam Brigades Abu Ubaida ya fitar da wata sanarwa da ke cewa “makiya na ci gaba da yin wasa da rayuwar sojojinsu da muka kama, suna yin watsi da bukatun iyalansu.”


Ya ce “da gangan Isra'ila ta kashe sojojinta uku jiya, inda ta zabi kashe su maimakon a sake su. Wannan zallan aikata laifi ne da ta dade tana yi kuma take ci gaba da yi game da mutanenta da ke tsare a Gaza.”


'Kisa bisa kuskure'


Ya ce Isra'ila ta "zaku ta kauce wa nauyin da ke rataye a wuyanta da kuma tasirin hakan.”


Ranar Juma'a Isra'ila ta sanar cewa "bisa kuskure" dakarunta sun kashe mutum uku da Hamas ta yi garkuwa da su a lokacin fada a yankin Shuja'iya da ke gabashin Birnin Gaza.


Kwarya-kwaryar binciken da sojoji suka yi, wanda kafafen watsa labaran Isra'ila suka wallafa ranar Asabar, cki har da gidan rediyon sojoji, ya nuna cewa sojojin sun nuna halayyar da "ba irinta" ta dace ba, abin da ya sa aka kashe wadanda ake tsare da su duk kuwa da cewa suna daga "fararen tutoci" a yankin na Shuja'iya.

Post a Comment

0 Comments