Jamhuriyar Benin za ta haɗa kai da ƙasashen da aka yi juyin mulki
Shugaban ƙasar Benin, Patrice Talon, ya ce ƙasarsa na fatan shiryawa da ƙasashe maƙwabta da aka yi juyin mulki na soja.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ƙasashen duniya ke Allah-wadai da juyin mulkin da ake yi a ƙasashen yammacin Afirka.
Shugaban ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a majalisar dokokin ƙasar kan halin da ƙasa ke ciki a ranar Alhamis.
Shugaba Patrice ya sake jaddada cewa ƙasarsa ba ta goyon bayan juyin mulki, sai dai : “Akwai lokacin suka da kuma lokacin buƙata, akwai kuma lokacin kau da kai da bayar da baya.”
"Ƙwatar mulki da bakin bindiga abu ne wanda duk masu kishin dumukuraɗiyya ke Allah-wadai da shi, mun yi hakan ne domin furta abin da ke cikin zuciyarmu daidai da al'adun ƙasarmu, mun yi haka ne tare da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, duk da haka ƙasar Benin ba ta da niyya ko fatan tsunduma al'umma cikin mawuyacin hali," cewar Shugaba Talon.
Akwai ƙasashe da dama a yammacin Afrika da suka fuskanci juyin mulki a baya-bayan nan da suka haɗa da Mali, da Guinea da Burkina Faso da kuma Nijar.
Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka Ecowas ta sanya wa Nijar takunkumai lamarin da ya haifar da rufe iyakarta da Benin.
“A bayyane ƙarara take, Benin ba ta taɓa fatan ƙasashe makwabta da hukumomin ƙasashen duniya su saka takunkuman da ka iya jefa al’umma cikin matsin rayuwa ba,” in ji mista Talon.
A baya-bayannan Ecowas ta yanke shawarar ci gaba da sanya wa Nijar takunkumai har zuwa lokacin miƙa mulki ga farar hula.
Mista Talon ya ce dole ne shugabannin riƙon su nuna wata shaidar da ke nuna goyon baya da hadin kai ga ƙungiyar Ecowas.
Jamhuriyar Benin dai na cikin ƙasashen da suka goyi bayan ƙaƙaba wa ƙasashen Mali da Guinea da Burkina Faso da kuma Nijar takunkumi bayan da sojoji suka karɓe mulki.
0 Comments