Jami’an tsaron farin kaya da Civil Defence a babban birnin tarayya Abuja, sun kama wasu mutane 82 da ake zargi da aikata barna da kuma masu hakar ma’adanai 22 ba bisa ka’ida ba daga watan Agusta zuwa yau.
Kwamandan hukumar NSCDC na babban birnin tarayya Abuja, Mista Olusola Odumosu ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ranar Alhamis a Abuja.
Odumosu ya ce an kama wasu mutane 20 da ake zargi da laifin satar rufa-ido da barnatar da muhimman kadarori da kayayyakin more rayuwa na kasa.
Ya ce an kama mutane biyar da ake zargi a watan Satumba da laifin lalata igiyoyin lantarki, 14 da laifin lalata wasu kadarorin jama’a da kuma wasu mutane biyu bisa zargin satar talabijin.
Kwamandan ya ce sauran wadanda ake zargin sun hada da wasu mutane 28 da aka kama bisa laifin lalata titin jirgin kasa da kuma lalata wasu muhimman kadarorin kasa. “An kama 11 a watan Oktoba da laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, In ji Shi.
0 Comments