Jam'iyyar APC mai mulki ta saka Abdul Samad Rabiu da Dahiru Mangal da A. A. Rano da wasu hamshakan 'yan kasuwa na Nijeriya a cikin kwamitin kudi na jam'iyyar, inda Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad ya ki karbar mukamin da ta ba shi.

Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad ya ki karbar mukamin da APC ta ba shi.



Jam'iyyar APC mai mulki ta saka Abdul Samad Rabiu da Dahiru Mangal da A. A Rano da wasu hamshakan 'yan kasuwa na Nijeriya a cikin kwamitin kudi na jam'iyyar.

Kamfanin BUA ya yi godiya ga APC bisa wannan karamcin sai dai ya ce babu ruwan kamfanin ko shugaban kamfanin da siyasa.


Shugaban kamfanin BUA a Nijeriya Abdul Samad Rabiu ya yi watsi da mukamin da aka ba shi na mamba a kwamitin kudi na Jam’iyyar APC.


Abdul Samad din ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da kamfaninsa na BUA ya fitar a shafin X inda ya ce babu wanda ya tuntube shi kafin a ba shi wannan mukamin.


A ranar Juma’a ne Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da sunayen mambobin kwamitocinta wadanda suka hada da na gudanarwa da kudi da watsa labarai da harkokin gwamnati da sasanci.


A cikin kwamitin na kudi, baya ga Abdul Samad, akwai sauran hamshakan ‘yan kasuwa na Nijeriya da ke cikin kwamitin irin su Dahiru Mangal da A. A Rano da Alhaji Mohammed Indimi.

Post a Comment

0 Comments