Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad ya ki karbar mukamin da APC ta ba shi.
Jam'iyyar APC mai mulki ta saka Abdul Samad Rabiu da Dahiru Mangal da A. A Rano da wasu hamshakan 'yan kasuwa na Nijeriya a cikin kwamitin kudi na jam'iyyar.
Kamfanin BUA ya yi godiya ga APC bisa wannan karamcin sai dai ya ce babu ruwan kamfanin ko shugaban kamfanin da siyasa.
Shugaban kamfanin BUA a Nijeriya Abdul Samad Rabiu ya yi watsi da mukamin da aka ba shi na mamba a kwamitin kudi na Jam’iyyar APC.
Abdul Samad din ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da kamfaninsa na BUA ya fitar a shafin X inda ya ce babu wanda ya tuntube shi kafin a ba shi wannan mukamin.
A ranar Juma’a ne Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da sunayen mambobin kwamitocinta wadanda suka hada da na gudanarwa da kudi da watsa labarai da harkokin gwamnati da sasanci.
A cikin kwamitin na kudi, baya ga Abdul Samad, akwai sauran hamshakan ‘yan kasuwa na Nijeriya da ke cikin kwamitin irin su Dahiru Mangal da A. A Rano da Alhaji Mohammed Indimi.
0 Comments