KISAN KIYASHIN BUHARI A ZARIYA: BAMU MANTA BA, BAMU YAFE BA. Inji Dr. Shamsudeen Hassan Zuru

 KISAN KIYASHIN BUHARI A ZARIYA: BAMU MANTA BA, BAMU YAFE BA.

Inji Dr. Shamsudeen Hassan Zuru.



Yau shekaru Takwas kenan cur, a irin wannan ranar ta 12 ga 12, 2015. Sojojin inada-kisa, Sojojinda ke kashe Mata da Yara a Ƙasar Hausa da sunan Ta'addanci, suka fito da maitarsu ƙarara, suka aukar da Kisan Kiyashi mafi muni a tarihin Kasar nan, da rana tsaka a Zariya.


Wasu sun ɗauka wai bisa Haɗari abun ya faru, sam ba haka bane, tsararren Shiri ne, wanda aka yi shekaru ana tsarawa, kuma ake neman yadda za a yi ya faru, ba tare da wata matsala ba. Shi ne suka laɓe da Ƙaryar tare hanya domin su aiwatar, karyarda har yanzu za ka ji wasu marasa kan gado daga cikin 'Yan Jaridu da sauran mutanen gari na yaɗawa, duk da an je kotun hukuma ta yi hukunci, ta ce ƙarya ne, ba a ma tare hanya ba, balle hayaniya, balle dukan Ƙirjin Soja, ta ce ƙarya ce kawai aka tsara, aka zartar, don haka a biya Diyyah.


 Amma har yanzu za ka ji wasu gauga'u da wasu makirai na cika baki suna cewa wai an tare hanya, ko hanyar Uwasu aka tare oho. An zo an yi wasa da Hankalin Al'umma domin a hanasu gane inda aka dosa, a hanasu tausayawa, su kuma ba su ankara ba. Kotun ƙasa ta ankarar da su,cewa ba a yi ba, amma har yau miyagun 'yan Jarida da Miyagun Malamai na masu wahayin Sheɗan.


To yanzu shi kisan Kiyashin Tudun Mauludi (Tudun Biri) da ya faru a satin da ya wuce, hanyar Uwarwa aka tare..? Iye..? Su suna kisan ne da manufa, amma kafin su yi za su samu wata ƙarya su fake da ita, domin a yita riritawa, kafin a gano gaskiya sai an dade, sai an sha wahala.


Yanzu a Tudun Mauludi ai da farko musawa suka yi, da suka ga 'Yan Uwa da Mutanen Kogo,da sauran masu Hankali sun dage ne sunata surutai a social media ne, sannan suka ce wai kuskure ne. Su so suka yi a yi shiru, sai abun ya wuce haka na. Kuma wallahi talnahi da mun yi shiru da yanzu sai dai guna guni, hatta malamanda ke cika baki yanzu daga dukkan ɓangarori, suna yi ne domin sun ga Arhar abun, domin sun ga hukuma ta yadda itace ta yi.


 Wallahi ,summa talnahi, da hukuma ta ja daga kamar yadda ta ja daga a kisrn Zariya, wallahi da mafi yawan waɗannan Lusaran Malaman muƙis za su yi. Ba muna rena abukda suka yi daga baya bane, amma kamata yayi tun ranar farko, tun awar farko, su zabura su mike, amma wasu ko tari basu yi ba sai bayan kwana biyu, wasu Uku. Wato sai da suka ga hanyar babu ƙaya sannnan suka ratsa.


Idan da za a yi Tambaya, a ce shin wai yaushe ne aka aukar da Kisan Kiyashi a Tudun Mauludi, wace rana ce aka tsara wannan abun, ? Amsa itace tun ranar 12 ga 12 2015. Aiwatarwa ne kawai ta faru a satin da ya wuce, amma tun a zariya aka zartar, aka buga sitamfi. Duk wani kisan Kiyashi da Kidnnaping da Banditry da ake yi a Arewa ta Yamma, ba a samu Lasisin farashi da tsananta shi ba, sai bayan da aka aukar kisan kiyashin Zariya.


Da suka kashe raunana a tsakiyar rana, kuma a tsakiyar Birni, suka ga an masu shiru, suka ga wasu na murna, suka ga wasu na zugawa, suka ga wasu na walima, sai suka ce, ashe Hausa Hankali bai isheta ba, ashe za mu iya aiwatar da Plan dinmu ba tare da tsrngwama ba.


To tun sannan farashin kashe Talaka a wannan yankin yayi arha. Tun sannan aka kashe 'yan mauludi a Tudun Biri. Dama itama ranar ranar 1 ce ga watan Maulidi, kuma an taru a zariya domin ɗaga tutar Maulidi.


Ba za a bar kisan babu Dalili a Arewa ba, har sai ranar da muka san ciwon kanmu, har sai ranar da muka san cewa da Hankali ake hukunci, da shi ake kallon Lamurra idan sun faru ba da Son rai ko son kai ba. Har sai mun san cewa Zalunci a kan Ɗaya, zalunci ne a kan kowa.


Kuma kowa ya sani har yanzu waɗanda aka kashe a zariya suna bin wannan Al'umma bashi. Bashin shi ne, su fito su yi tofin Allah tsine da wannan Aika-aika kamar yadda da yawansu suka giyi baya, kamar yadda da yawansu suka yi shiru a lokacin, kuma su nemi gafarar 'Yan Harka Islamiyyah da Jagiron Harka Islamiyyah. Wannan hakki ne a kan wuyan duk wani Dan kasar nan.


Idan ba haka ba, to Allah dai ba Azzalumi bane. Idan ka yiwa wani Izgili, to zai kawo ranar da wasu za su.maka kaima. Kuma wallahi matukar Al'umma bata barranta da bannar da aka yi a zariya ba, to wallahi ba za ta taɓa ganin daidai ba. Jinin nan zai yita bibiyarta har sai ya leƙa gidan kowa. Wannan ba mummunar fata bace.haka sunnar Allah take.


Shamsudeen Hassan Zuru

12/12/2023

Post a Comment

0 Comments