Kungiyar Malaman Musulunci ta duniya ta yi kira a yi zanga-zanga a fadin duniya don neman tsagaita wuta a Gaza

 Kungiyar Malaman Musulunci ta duniya ta yi kira a yi zanga-zanga a fadin duniya don neman tsagaita wuta a Gaza.



Kungiyar Malaman Musulunci ta duniya ta yi kira a gudanar da zanga-zanga a fadin duniya a ranar Litinin domin tilasta wa Isra'ila daina luguden wuta a Gaza.


Sanarwar da kungiyar ta fitar ta yi kira ga jama'a a fadin duniya, musamman Musulmai, su shiga zanga-zangar sannan ta nemi manyan kungiyoyin dunuya da jam'iyyu da mutane masu fada-a-ji su ci gaba da yin zanga-zanga har sai lokacin da Isra'ila ta daina kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza.


Ta ce ta lura da yadda kaurace wa kayan Isra'ila da kuma yunkurin kai kayan agajin jinkai suka yi tasiri amma duk da haka ta nuna gazawar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wurin tsayar da yakin.


Kungiyar ta bayar da shawarar sauya tsarin hawa kujerar-na-ki na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, tana mai cewa ya kamata tsarin ya kasance bisa yawan kuri'un da aka kada.


Ali al Qaradaghi, Sakatare Janar na kungiyar, ya jaddada cewa za su yi zanga-zargar ce domin goyon bayan Falasdinawa da kuma kira ga kasashen duniya su matsa lamba don daina yaki a Gaza.

Post a Comment

0 Comments