Kusan Falasdinawa miliyan 1.9 sun rasa matsugunansu a fadin Gaza.

 Kusan Falasdinawa miliyan 1.9 sun rasa matsugunansu a fadin Gaza.



Kusan Falasdinawa miliyan 1.9 sun rasa matsugunansu a fadin Gaza - MDD

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 59 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falaadinawa fiye da 15,523, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 41,316 sun jikkata.

Kamfanonin sadarwa na Falasdinawa sun ce an katse ayyukan sadarwa a Gaza gaba daya saboda hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da yi.


Kusan Falasdinawa miliyan 1.9 sun rasa matsugunansu a fadin Gaza - MDD


Kusan mutane miliyan 1.9, ko sama da kashi 80 na al'ummar kasar, sun rasa matsugunansu a fadin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, in ji hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu, UNRWA.


Ya kara da cewa, ya zuwa ranar 2 ga watan Disamba, ma'aikatan UNRWA 111 ne aka kashe tun farkon yakin Isra'ila a kan yankin Falasdinu.


Da sanyin safiyar Juma'a ne sojojin Isra'ila suka sake kai hare-hare a Zirin Gaza bayan ayyana kawo karshen dakatar da ayyukan jinƙai na tsawon mako guda.


 Hare-haren Isra'ila a Gaza 'na ƙara tsananta ga yara da iyaye mata': UNICEF




Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 509 sannan ta jikkata mutum 1,316 tun daga ranar Juma'a, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza.


Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda tashe-tashen hankula ke ƙara ƙamari a yankin kudancin Gaza, inda mai magana da yawunsa ya ce hare-haren suna da muni kamar yadda aka sha fama da su a arewacin kasar.


"Duk da abin da aka tabbatar, hare-haren da aka kai a kudancin Gaza suna da muni kamar yadda ya faru a arewa. Ko ta yaya, abin yana kara ta'azzara ga yara da iyaye mata," in ji mai magana da yawun UNICEF James Elder a ranar Litinin a X.


"Muryarku tana da mahimmanci. Dole ne mu yi imani cewa za mu iya zama wani bangare na dakatar da yakin da ake yi a kan yara... Yin shiru ba zai yi mana komai ba," in ji shi.


Da sanyin safiyar Juma'a ne sojojin Isra'ila suka sake kai hare-hare a Zirin Gaza bayan ayyana kawo karshen tsagaita wuta da aka yi na tsawon mako guda.


 Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa 30 a arewacin Gaza


Kamfanin dillancin labaran Falasdinu ya rawaito cewa aƙalla mutum 30 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a arewacin Gaza.


Gaba daya Falasdinawa 15,899 ne aka kashe a hare-haren Isra'ila a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, kashi 70 cikin 100 cikinsu mata ne da ƙananan yara, in ji kakakin ma'aikatar lafiya ta Falasdinu da ke Gaza.


Sojojin Isra'ila za su yi 'yaki sosai' a kudancin Gaza


Rundunar sojin Isra’ila ta ce an an raunata sojojinta uku a wani hari da aka kai musu daga kasar Lebanon a wani sansaninsu da ke arewacin Isra’ila.


Isra’ila ta ce an harba musu rokokin ne a a yayin da sojojinta ke a sansaninsu da ke birnin Yiftah, inda ta ce sojojin nata sun mayar da martani ta hanyar harba makamai daga gefen da harin ya fito.



Sojojin Isra'ila na ci gaba da kashe Falasdinawa da ke Gaza.

Ana samun rikici tsakanin sojojin Isra’ila da kuma mayakan Hezbollah na Lebanon inda suke ci gaba da kai wa juna hari tun bayan da aka soma rikici tsakanin Gaza da Isra’ila.


Qatar za ta ci gaba da kokarin dawo da tattaunawar sulhu don tsagaita wuta a Gaza: Firaiminista



Qatar za ta ci gaba da kokarinta da sauran kasashen duniya na dawo da tattaunawar sulhu don tsagaita wuta a Gaza da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta


Firaiminista kuma Ministan Harkokin Waje Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani ya bayyana a cikin jawabinsa yayin taron Majalisar Ministoci karo na 158 na zaman taro na 44 na kasar Qatar ya ce: "Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta sanar da cewa, an gudanar da taron koli na kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf (GCC) a birnin Doha."


Al Thani ya sake nanata cewa "Qatar ta yi Allah wadai da laifuffukan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta aikata tare da yin kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa cikin gaggawa ba tare da nuna son kai ba kan wadannan laifuka, musamman hare-haren da aka kai kan fararen hula, da agaji da wuraren jinkai."

Post a Comment

0 Comments