Majalisar Dokokin Denmark ta haramta kona Alkur’ani.

 Majalisar Dokokin Denmark ta haramta kona Alkur’ani.

Bayan an yi zazzafar muhawawa a zauren majalisa, ‘yan majalisa 94 sun amince da kudurin dokar yayin da ‘yan majalisa 77 suka yi watsi da shi a majalisar dokokin mai mambobi 179.

Majalisar Dokokin Denmark ranar Alhamis ta haramta kona Alkur’ani mai tsarki tana mai cewa laifi ne "waulakanta rubuce-rubucen masu muhimmanci da wasu al’ummomi mabiya addini suke girmamawa."

Bayan an yi zazzafar muhawawa a zauren majalisa, ‘yan majalisa 94 sun amince da kudurin dokar yayin da ‘yan majalisa 77 suka yi watsi da shi a majalisar dokokin mai mambobi 179.

Kudurin dokar ya haramta konawa d yagawa da kuma wulakanta littafin mai tsarki a bainar jama'a ko a shafukan intanet da kuma nuna yin hakan ga duniya.

Za a yanke wa wanda aka samu da laifin wulakanta Alkur'ani daurin shekara biyu a kurkuku ko a ci tararsa.

Duk da yake jam'iyyu uku da ke cikin gamayyar gwamnatin kasar sun goyi bayan kudurin dokar, babu wani mamba na gamayyar da ya tsaya domin mayar da martani kan masu adawa da kudurin lokacin muhawara a zauren majalisar.

Jam'iyyar Social Liberals (Radikale Venstre) ita ce jam'iyyar adawa kadai da ta goyi bayan kudurin dokar.

Post a Comment

0 Comments