Masu neman a zauna lafiya sun yi gagarumar zanga-zanga a Amurka kan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.
Wata kungiyar Yahudawa da ke neman Isra'ila ta daina kai hare-hare a Gaza ta gudanar da jerin zanga-zanga a birane takwas na Amurka ranar Alhamis a kwana na takwas na bikin al'adun Yahudawa mai suna Hanukkah, inda suka toshe hanyoyi da gadoji a biranen Washington da Philadelphia.
A Washington, kungiyar Yahudawa ta Jewish Voice for Peace ta ce masu zanga-zanga kimanin 90 sun toshe wata babbar hanya a yankin New York Avenue da ke arewa maso yammacin babban birnin kasar. 'Yan sanda sun ce masu zanga-zangar sun toshe wasu manyan tituna na New York Avenue da North Capitol Street sannan suka bukaci mutane su yi amfani da wasu hanyoyin.
"A dare na 8 na bikin Hanukkah, a birane 8 da kuma gadoji 8," in ji kungiyar Jewish Voice for Peace a sakon da ta wallafa a shafinta na X, wanda a baya ake kira Twitter.
"Mun taru a nan, da kuma a fadin kasar nan, inda muke da yawa, kuma muna cewa ba mu yarda a ci gaba da kai hare-hare ba."
An yi manyan gangami a Boston, Atlanta, Chicago, Minneapolis, Seattle da Portland da Oregon.
'A bar mutanen Gaza su sarara'
A Philadelphia, masu zanga-zanga kusan 200 sun toshe manyan hanyoyi masu lamba I-76, amma an kama mutum fiye da 30, kamar yadda wani ganau ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Masu zanga-zangar sun rike kwalaye da aka rubuta cewa: "A bar mutanen Gaza su sarara" da kuma "Ba da yawunmu ake yaki ba."
Ranar Talata Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Isra'ila ta gaggauta tsagaita wuta a hare-haren da take kai wa Gaza.
0 Comments