Mun kashe karin sojojin Isra'ila 20 tare da jikkata wasu a Gaza: Al Qassam Brigades

 Mun kashe karin sojojin Isra'ila 20 tare da jikkata wasu a Gaza: Al Qassam Brigades.



Al Qassam Brigades, wanda shi ne bangaren sojoji na kungiyar Hamas, ya dakarunsa sun kashe sojojin Isra'ila sama da 20 tare da jikkata da dama a wani gumurzu da suka yi a Birnin Gaza.


A wani sako da ya wallafa a manhajar Telegram, Al Qassam Brigades ya ce mayakansa sun yi arangama da dakaru na musamman na Isra'ila da ke “kutsawa yankin Sheikh Radwan da ke Birnin Gaza, lamarin da ya kai ga kisan sojoji fiye da 20 tare da jikkata wasu.”


A wani sako na daban, bangaren sojin na Hamas ya ce mayakansa sun kai hari kan “tankar yakin Isra'ila ta Merkava da abubuwan fashewa na Sho'ath a yankin Sheikh Radwan na Gaza.”


Kazalika mayakan Al Qassam Brigades sun yi amfani da makamai masu linzami suka ragargaji “wani jerin gwanon ababen hawa na Isra'ila da kuma sojojin kasar a birnin Khan Yunis na kudancin Zirin Gaza.”

Post a Comment

0 Comments