Mun kashe 'yan ta'adda sama da 6,000 a 2023: Hedikwatar Tsaron Nijeriya


Mun kashe 'yan ta'adda sama da 6,000 a 2023: Hedikwatar Tsaron Nijeriya.



Sojojin  Nijeriya sun ce baya ga 'yan ta'addan da suka kashe, sun kama mutum 6,970 wadanda ake zargi da ayyukan ta’addanci.

Sojojin sun ce sun ceto sama da mutum 4,000 wadanda aka yi garkuwa da su a 2023. / Hoto: NA

Rundunar Tsaron Nijeriya ta ce a yakin da take yi da ta’addanci a fadin kasar, ta yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 6,886 a fadin kasar.


Daraktan watsa labarai na Hedikwatar Tsaron Nijeriya Manjo Janar Buba Edward ne ya bayyana haka a Abuja a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja a ranar Juma’a.


Ya bayyana cewa sojojin Nijeriya a shekarar 2023 sun yi abin a yaba domin kuwa baya ga ‘yan ta’addan da suka kashe, sun kama mutum 6,970 wadanda ake zargi da ayyukan ta’addanci.


Haka kuma hedikwatar tsaron ta ce sojojin kasar sun yi nasarar kwato mutum 4,488 wadanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a fadin kasar.


A yayin jawabin, Manjo Janar Buba, ya bayyana cewa sojojin sun yi nasarar kwato litar danyen man fetur miliyan 100 wadda aka sace da kuma lita miliyan 60 ta man dizel.


Manjo Janar Buba ya bayyana cewa a shekarar 2023, ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da masu satar mai da ‘yan aware da kuma rikici tsakanin manoma da makiyaya su ne laifukan da suka fi yaki da su.


Ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun fi addabar Arewa Maso Tsakiya da Arewa Maso Yammacin Nijeriya sannan kuma ‘yan Boko Haram da ISWAP sun fi addabar Arewa Maso Gabashin Nijeriya.


A cewarsa, babbar barazana a Kudu Maso Gabas da Kudu Maso Yammacin Nijeriya ita ce ta ‘yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar BIAFRA da ta masu fafutukar kafa kasar Yarabawa.

Post a Comment

0 Comments