“Na ji dadi da na karbi Addinin Musulunci. Ina samun farinciki da kwanciyar hankali. ” in ji Liliana Baturiya yar shekara 62 data sauke alqur'ani a Kano.

 “Na ji dadi da na karbi Addinin Musulunci. Ina samun farinciki da kwanciyar hankali. Sannan saukar Alqur’ani din nan ma ta bani farinciki. “Alqur’ani littafi ne mai dadi kuma shi ne ya ke zame min jagora a rayuwa ta a halin yanzu. Zan ci gaba da kokarin yin hadda, duk da cewa dai na tsufa,” in ji Liliana.



Asalinta


Ainihinta 'yar ƙasar Bulgaria ce, kuma aure ne ya kai ta Kano. A yanzu, Liliana tana da shekara 62 a duniya. Kuma in ji ta, abubuwa da yawa ne ke burge ta game da Kano, mazauninta na yanzu.


A cewar jaridar Daily Nigerian ta intanet, Baturiyar ta zo Kano ne fiye da shekara 30 a baya, sa'ar da ta auri wani ɗan kasuwa wanda Allah ya yi masa rasuwa yanzu, marigayi Ibrahim Sambo a can ƙasarta ta haihuwa Bulgaria.


Kuma dattijuwar tana 'ya'ya biyu.


Liliana Mohammed ta yi bikin saukar Kur'ani ne, tare da sauran ɗaliban makarantar Islamiyya ta Manba’irrahman a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba.


Ta ce yanayi a birnin Kano, na da ƙarfafa gwiwar ayyukan ibada na addinin Musulunci, musamman idan ta kwatanta da ƙasar da ta fito.


"Ta fuskar lokaci. Lokutan sallah da na azumi sun dace matuƙa. Tsawon dare da na rana, kusan ɗaya ne. Ba kamar wani sashen na duniya ba, inda ake da sa'a biyar kawai a lokacin dare."


Ta ce shi kansa tsarin muhalli a Kano, yana da burgewa da ƙarfafa gwiwa. A lokacin kiran sallah, duk inda mutum yake zai ji, in ji Baturiyar. Kuma hakan, a cewarta abin ƙarfafa gwiwa ne, sannan ga mutane a ko'ina suna sallah a lokacin.

Post a Comment

0 Comments