NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben Kodin kusan 100,000
Hukumar ta ce ta kuma kama wata dattijuwa mai shekara 70 tare da danta da kilo 117.900 na wiwi.
Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce ta yi kamen miyagun kwayoyi masu dumbin yawa daf da Bikin Kirisimeti.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa daga cikin miyagun kwayoyin da ta kama har da kwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben maganin tari mai dauke da kodin kusan 100,000.
Hukumar ta ce ta kama kwayoyin na Tramadol a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas tare da da hadin gwiwa da jami’an kwastam da sauran jami’an tsaro.
Hukumar ta ce an shigo da kwayoyin ne daga birnin Hamburg na Jamus. A cewar sanarwar, kwayoyin na cikin manyan kwalaye 100 wadanda baki dayansu nauyinsu ya kai kilo 7,150.
Haka kuma hukumar ta ce jami’anta da ke aiki a Legas sun kai wani samamen a wasu shaguna biyu a ranar Laraba 20 ga watan Disamba a kasuwar duniya da ke yankin Ojo.
0 Comments