Netanyahu ya ce dole Isra'ila ta kwace ikon gudanar da iyakar Gaza da Masar.
Firaiministan Isra'ila Benjamin NetanyahuFiraiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin sake kwace ikon gudanar da iyakar Gaza da Masar, a yayin da adadin Falasdinawan da dakarunsa suka kashe ya zarta 21,670.
"Yakin nan ya kai kololuwa," in ji Netanyahu a hira da manema labarai, inda yake magana a kan ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta kai harin ba-zata Isra'ila inda ta kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da mutum 240.
Ya kara da cewa dole ne yankin Philadelphi da ya ratsa iyakar Gaza da Masar ya kasance a hannun Isra'ila.
"Dole a toshe yankin," a cewar Netanyahu. "A bayyane yake cewa babu wani shir da zai kawar da hare-haren da muke so a daina kaiwa."
0140 GMT — Ministan Tsaron Isra'ila ya ki halartar taron manema labarai da Netanyahu
Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant da Ministan da ke Jagorantar Yaki Benny Gantz sun ki halartar taron manema labarai da Firaiminista Benjamin Netanyahu ya gudanar ranar Asabar da maraice.
Hukumar watsa labarai ta Isra'ila ta wallafa sako a shafin X da ke cewa Gallant da Gantz sun ki halartar taron ne ba tare da bayyana dalilin hakan ba.
Babu wata sanarwa da mutanen uku suka fitar a game da wannan batu, ya zuwa karfe shida da minti arba'in a agogon GMT.
0 Comments