NIJAR DA BURKINA FASO SUN JANYE DAGA KAWANCEN KASASHE BIYAR DAKE YAKI DA TA'ADDANCI A YANKIN SAHEL.

 Nijar da Burkina Faso sun janye daga kawancen G5 Sahel na Faransa kan yaki da ta'addanci

Nijar da Burkina Faso sun janye daga kawancen G5 Sahel na Faransa kan yaki da ta'addanci.

Mali ce ta soma janyewa daga kawancen kasashe biyar da ke yaki da ta'addanci a yankin Sahel.



Burkina da Nijar sun ce kungiyar G5 Sahel ba ta taka rawar da aka kafa ta don ta yi 

Shugabannin rundunonin sojin Burkina Faso da Nijar a ranar Asabar sun ce sun janyewa daga kawancen kungiyar G5 Sahel ta kasashe biyar da ke yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel, lamarin da zai haifar da gagarumin koma-baya kan yaki da ta'addanci a yankin.


Kungiyar ta G5 Sahel, wadda aka kafa a 2014, ba ta taka rawar gani sosai ba, inda a bara Mali ta fice daga cikinta bayan sojoji sun yi juyin mulki a kasar.


A shekarar 2017 ne shugabannin kasashen biyar tare da goyon bayan Faransa suka amince su tura tawaga daya ta jami'an tsaro na hadin gwiwa domin fatattakar 'yan ta'adda a yankin, amma yanzu sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina da Nijar da Mali dukkansu sun zargi Faransa da yin shisshigi a cikin lamarin bayan da ta tura karin dakarunta yankin na Sahel.

Burkina da Nijar "sun yanke shawarar cin gashin kansu inda suka janye daga kungiyar G5 Sahel, ciki har da dauke dakarunsu" daga ranar 29 ga watan Nuwamba, kamar yadda kasashen biyu suka bayyana a sanarwar hadin gwiwa.


'Gaza cim ma nasara'


"Kungiyar ta gaza cim ma nasara. Abin takaicin ma shi ne, babban burin kasashenmu na tabbatar da tsaro da ci-gaba a yankin G5 Sahel, ya fuskanci tarnaki daga gwamnatocin da suka gabata, abin da ya tabbatar mana cewa bukatarsu ba ta dace da tsarinmu na samun 'yanci da kamala, kamar yadda aka fayyace a shirin na G5 tun da farko," in ji sanarwar.


A wani jirwaye mai kamar wanka da suka yi wa Faransa, kasashen biyu sun kara da cewa "bai zai yiwu kungiyar G5 Sahel ta rika cika muradin kasashen waje ba, alhali al'ummominmu suna shan wahala, kuma ana ba mu umarni kamar wasu kananan yara, a hana jama'armu 'yanci."

Post a Comment

0 Comments