Nijeriya na kara jaddada kira kan a saki tsohon shugaban Nijar da aka hambarar Mohamed Bazoum, tare da rokon sojojin da ke mulkin kasar kan su bar shi ya tafi kasar da yake so.
Nijeriya ce a halin yanzu ke jagorantar kungiyar ECOWAS wadda ta saka wa Nijar din takunkumi tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a watan Yuli.
ECOWAS ta jima tana son a saki Bazoum nan take domin komawa kan kujerar shugabanci, sai dai sojojin da ke mulkin kasar na ci gaba da tsare shi inda sojojin suka ce za a iya shafe shekara uku kafin a koma kan mulkin dimokuradiyya a kasar.
“Muna son a saki Shugaba Bazoum ta yadda zai iya barin Nijar,” kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar ya shaida wa kafar watsa labarai ta Channels a Nijeriya.
‘Cire takunkumi ‘
“Ba zai ci gaba da zama a tsare ba. Zai tafi wata kasa wadda aka amince. Daga nan ne za mu fara magana kan batun cire takunkumi.” Ya bayyana cewa har yanzu ECOWAS a shirye take domin tattaunawa da sojojin Nijar.
“Kun san cewa damar na nan. A shirye muke a ko da yaushe, za mu iya sauraren su, wuka da nama na hannunsu.”
Shugabannin ECOWAS za su yi taro a Abuja babban birnin Nijeriya a ranar 10 ga watan Disamba domin tattaunawa kan batun yankin, wanda ya kasance yana fusknatar juyin mulkin soji tun daga shekarun 2020, kama daga Mali zuwa Burkina Faso da Guinea da Nijar.
‘Yunkurin juyin mulki’ a Saliyo da Guinea-Bissau
A watan da ya gabata, wani yunkurin juyin mulki a Saliyo ya yi sanadin mutuwar mutum 21, kamar yadda manyan jami’an gwamnatin kasar suka tabbatar a kasar wadda ke cikin kasashen ECOWAS.
Ita ma Guinea-Bissau wadda kasa ce ta ECOWAS, shugabanta Umaro Sissoco Embalo a ranar Asabar ya ce rikicin da aka yi a wannan makon wanda a ciki akwai wasu daga cikin dogaran kasar “yunkuri ne na juyin mulki.”
0 Comments