Sanata Barau Zai Ɗauki Nauyin Karatun Ɗaliban Da Su Ka Kammala Digiri Da Daraja Ta Ɗaya, Zuwa Ƙetare

 Mataimakin shugaban Majalissar Dattijai ta ƙasa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewar tuni shirye-shirye su ka yi nisa, na fara bayar da tallafin karatun Digiri na biyu, zuwa ƙasashen ƙetare, ga Ɗaliban yankin da ya ke wakilta, da su kammala Digirinsu na farko da daraja ta ɗaya (First Class).



Sanata Barau, ya bayyana hakan ne, ya yin da ya karɓi baƙuncin shugabancin ƙungiyar Ɗalibai ta SUG, reshen Jami’ar Bayero, a Majalissar ta Dattijai.


Ya ce, za a biyawa ɗaliban su karanta fannonin fasahar zamani, irin su: Na’ura mai tunani irin na Ɗan Adam, Fasahar Sarrafa Bayanai, Fannin ƙirƙire-ƙirƙire, da makamantansu.


Ya kuma ce, zai ɗauki nauyin karatun ne, ta ƙarƙashin gidauniyarsa ta Barau Jibrin Foundation.


A nasu ɓangaren, shugaban ƙungiyar Ɗaliban ta SUG, Auwalu Lawal Nadabo, tare da Mataimakiyarsa, Naja’atu Muhammad, godewa Sanatan su ka yi, bisa ƙoƙarin da ya ke na ganin an magance ƙalubalen da fannin Ilimi ya ke fuskanta, da ma wannan gagarumin yunƙuri nasa.

Post a Comment

0 Comments