Saudi Arebiya ta shiga jerin ƙawayen Amurka wurin kaiwa Dakarun Yaman hari, wadda aka san su da ƴan Houthi da suka datse Ruwan Maliya.

 Saudi Arebiya ta shiga jerin ƙawayen Amurka wurin kaiwa Dakarun Yaman hari, wadda aka san su da ƴan Houthi da suka datse Ruwan Maliya.



Wannan ƙawancen, Amurka ne ta naima daga sashin ƴan uwanta turawa da wasu rukunin larabawa da take juya akalar su, akan suzo ai gamayyar murkushe Dakarun Musulunci na Yaman ɗin daga farmakin da suke kaiwa kan Jiragen ruwa na Kasuwan Isra'ila, da kuma wadda zasu kaiwa Isra'ila kaya ko daga wace ƙasa ne.


Dakarun Musuluncin na Yaman sunce wannan matakin, sun dauke shine don dakile hare-haren da Isra'ila take kaiwa kan yara da mata a Gaza tare da rubde gidajen su, wuraren cin Abinci da kuma Makarantu zuwa Masallatai da Cocina.


Sunce zasu cigaba da wannan Hare-haren har sai komi ya lafa a Gaza dake Falasdinu, sannan su janye kudiri da Makaman su, ko kuma su kansu Falasdinawa a Hukumance suce basa bukatar abinda Yaman take na tallafa musu, sai su janye kai hare-haren. 


Wannan shine dalilin da yasa Amurka ta naimi hadakar ƙasashen dake Iyaka da Yaman akan su basu goyon baya wurin murkushe Dakarun na Musulunci, yanzu haka Saudi Arebiya ta shiga jerin ƙasashen da zasu farmaki Dakarun na Musuluncin, saboda hare-haren da suke kaiwa ƙasar ta Isra'ila da kuma duk wani jirgin kasuwanci na ruwa da zai kai musu kaya zuwa ƙasar. 


Muhd Bala Afuwa

Post a Comment

0 Comments