Shari’ar Dauda Kahutu Rarara a kotu na cigabaa da daukar hankali.

 Shari’ar Dauda Kahutu Rarara a kotu na cigabaa da daukar hankali



Kotun Majistiri mai lamba 1, da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa ta ɗage lokacin cigaba da sauraron ƙarar da Fitaccen Ɗan Jaridar nan, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya shigar da Mawaƙi Rarar a gabanta, zuwa ranar 8 ga watan Janairun 2024.


Kotun ta sanar da ɗage lokacin cigaba da sauraron shari’ar ne, da safiyar yau, bayan hallarar Lauyoyin ɓangarorin guda biyu, na mai ƙara da wanda ake ƙara a gaban Kotun, duba da kasancewar yau Litinin 4 ga watan Disamba, a matsayin ranar da Kotun ta sanya, domin cigaba da sauraron shari’ar, sai dai taron Lauyoyi da ake gudanarwa (Law Week) ya kawo cikas ga gudanar da zaman Kotun, bayan da Hukumar Shari’a ta ƙasa ta umarci Kotuna da kada su saurari shari’u a yau, domin bawa Lauyoyi damar halartar wannan taro.


Wannan zaman da ke a matsayin na biyu, a shari’ar kuma, shi ne ya kasance na farko da lauyoyin Mawaƙi Rarara su ka halarci Kotun, duba da yadda su ka bijirewa halartar zaman farko, bisa dalilin rashin isar takardar sammaci gare su.


Jagoran Lauyoyin da ke kare Mawaƙi Rarara, Barista A.I Ma’aji, ya ce rashin sanin ana shari’ar ne ya hanasu halarta, amma yanzun sun amsa gayyatar Kotu, bayan da aka liƙe sammaci a gidan Rararan, wanda ya alamta musu cewar ana shari’a da shi.


A nasa ɓangaren, Lauyan mai ƙara, Barista Muhammad Barde Abdullahi, ya ce shari’ar ta ƙunshi zargin aikata manyan laifuka, dan haka wajibi ne, Mawaƙin ya halarci zaman Kotun, ba wai turo iyakacin Lauyoyinsa ba, kuma za su san abin da ya kamata su yi, idan Kotun ta sake zama.


Wani Ɗan Jarida, mai suna, Alhaji Sani Ahmad Zangina ne dai, ya maka Mawaƙin a gaban Kotu, bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya jawo tunzuri a tsakanin al’umma, bayan da ya zargi Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da damalmala al’amuran ƙasar nan, kafin miƙata ga sabon shugaban ƙasa na yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.



Post a Comment

0 Comments