Sojojin Isra'ila sun sace Falasdinawa sannan suka yi musu zigidir a Gaza da aka mamaye
Bidiyoyin sun nuna yadda dakarun Isra'ila suke wulakanta wasu Falasdinawa fararen-hula a arewacin Gaza, a wani yanayi mai kama da abin da ya faru lokacin Nazi a Jamus.
Kafafen watsa labaran Isra'ila da na Falasdinu sun fitar da wasu bidiyoyi da ke nuna wasu maza Falasdinawa zigidir a tsare a hannun sojojin Isra'ila, inda wata jarida da ke London ta ce dan jaridarta na cikin wadanda dakarun Isra'ila suka yi wa wannan wulakanci.
An yi ta yada bidiyoyin a soshiyal midiya ranar Alhamis, kuma wani bincike da kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi kan bidiyoyin ya nuna cewa an dauke su ne a garin Beit Lahia da ke arewacin Gaza da Isra'ila ta mamaye, ko da yake yana da wahala a san takamaimai unguwar da aka dauke su.
Daya daga cikin bidiyoyin ya nuna hannun wani soja, abin da ke nuna cewa daya daga cikin sojojin mamaya ne suka dauki bidiyon.
A wani bidiyon, an nuna dandazon Falasdinawa maza da aka rufewa idanu sannan aka zaunar da su hannayensu a daure a bayansu yayin da su kuma sojojin Isra'ila suke kallonsu.
Osama Hamdan, wani mamba na bangaren siyasa na kungiyar Hamas, ya yi Allah wadai da wannan "cin mutunci na fararen-hula da ba sa dauke da makamai wadanda ba su da alaka da yakin da Isra'ila take yi."
Wasu Falasdinawa sun gane 'yan'uwansu a cikin bidiyoyin kuma sun ce ba su da wata alaka da Hamas da ma duk wata kungiya.
Hani Almadhoun, wani Ba'amurke dan asalin kasar Falasdinu da ke zaune a Virginia, ya ga 'yan'uwansa a cikin bidiyon kuma ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "fararen-hula ne da ba su da alaka da Hamas ko ma duk wata kungiya."
"Sun dauke su daga gidan wani dan'uwansu da ke kusa da kasuwa. Sun tsare dan'uwana Mahmoud, mai shekara 32, da dansa Omar, dan shekara 13, da wani dan'uwana Aboud, mai shekara 27, da kuma mahaifina mai shekara 72, da surukaina da dama."
Fararen-hula aka kama
Lokacin da aka tambayi kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari game da bidiyoyin, ya yi ikirarin cewa "masu ta'addanci ne suke yin saransa".
Sai dai jaridar Al-Araby al-Jadeed, wato The New Arab, da ke da hedkwata a London, ta ce daya daga cikin mutanen da ke cikin bidiyon wakilinta ne na Gaza mai suna Diaa al Kahlout, kuma an kama shi ne tare da fararen-hula da wasu 'yan'uwansa.
"Al Kahlout na cikin gomman mazauna Gaza da dakarun Isra'ila suka kama sannan suka tilasta musu tube tufafinsu inda suka wulakanta su bayan sun kai su wani wuri da ba a sani ba, kamar yadda ganau suka tabbatar," in ji jaridar.
0 Comments