Taƙaitaccen Tarihin Ahmed Musa MON
Ahmed Musa mai shekaru 30, Ɗan asalin ƙasa Nigeria, Wanda ke fafata wasa a ƙungiyar Sivasspor ta ƙasar Turkiyya da kuma Super Eagles ta ƙasa Nigeria a matakin ƙasa.
An haifi Ahmed Musa a ranar 14 ga watan Oktoba 1992, a birnin Jos dake Jihar Plateau, Nigeria a cikin Dangi mabiya addinai da yawa. Mahaifiyarsa Sarah Musa (née Moses) Kiristace ƴar Jihar Edo dake Kudancin Nigeria, Yayin da mahaifin sa Musulmi ne daga Arewacin Nigeria.
Musa yayi karatun Firamare ɗin sa ne a Saint Peace Primary kafin ya koma Ihya'ul Islmic Secondary School Inda yayi karatun Sikandire ɗin sa a can. Daga nan koma ya koma GBS Football Academy, Inda daga nan rayuwar ƙwallon ƙafar sa ta fara.
Ɗan wasan na ƙasa Nigeria ansan shi da aiki tuƙuru a cikin fili, Mafi yawa idan yana buga wasa a gefen hagu. Ahmed Musa ya fara ya Musa hazo ne a gasar Lig ɗin Nigeria NPFL a kakar wasan 2009 zuwa 2010 lokacin da yake buga wasa a Kano Pillars.
Tun daga nan Ahmed Musa ya fafata wasanni da dama a ƙungiyoyi daban-daban a nahiyar Turai ciki harda ƙungiyar gasar Premier League Leicester City. Sannan ya samu nasarori a matakin ƙasa. Inda ya kafa tarihin zama ɗan wasa mafi yawan buga wasanni a Super Eagles ta ƙasa Nigeria.
Ahmad Musa ya fara rayuwar sa ta ƙwallon ƙafa ne a GBS Football Academy inda yayi wasa a ƙungiyar daga shekarar 2005 zuwa 2008. A 2008 ya koma zaman aro zuwa ƙungiyar JUTH. A lokacin kakar wasan 2009 zuwa 2010, Ahmed Musa ya koma zaman aro a Kano Pillars. A Pillars ɗinne ya kafa tarihin zura ƙwallaye 18 a wasanni 25.
Daga nan ne ɗan wasan gaban na Super Eagles ya samu komawa ƙungiyar ƙasar Holland VVV Venlo, Inda ya fafata musu wasa daga shekarar 2010 zuwa 2012. Ahmed Musa ya samu babbar nasarar sa ne a rayuwar sa ta ƙwallon ƙafa a Kulab, A ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta CSKA Moscow inda ya zura ƙwallaye 42 a wasanni 125 lokacin da yake bugawa ƙungiyar ta ƙasar Russia a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2016.
Tarihi bazai manta ƙwallayen da Ahmed Musa ya zurawa ƙasar Argentina ba a gasar cin kofin Duniya ta shekarar 2014, Da kuma ƙwallayen da ya zurawa ƙasar Iceland a gasar cin kofin Duniya ta shekarar 2018.
• Fagen Wasanni
0 Comments