Tarihin Gwagwarmayar sarkin Musulmi Attahiru I da Turawan Mulkin Mallaka kashi na Daya.

Tarihin Gwagwarmayar sarkin Musulmi Attahiru I da Turawan Mulkin Mallaka kashi na Daya.



Shekuru dari da ashirin dai-dai da shahadar sarkin musulmai Attahiru. Wanda turawan mulkin-mallaka suka kashe a gumurzun da suka ruhuta cewa ba su ga irinsa ba a yawonsu na mamayar mulkin-mallaka. Anyi gumurzu ne a garin Bormi. Bayan wata tafiya ta kunar bakin-wake daga sakkwato zuwa garin.


Labarin sarki Attahiru yana daga cikin hikayoyi masu darasi. Wadanda ya kamata a sani domin amfani da darussan a aikace. Tarihi wani abu ne wanda Al’ummar da ta san inda kanta ke mata ciwo take runguma da tarairaya tana aiki da shi sosai.


Al’amura da raneku irin na shaikh Attahiru suna da muhimmanci sosai. Ana haska su a kuma kalli gaba da fitilarsu. Amma Sam al’ummar musulmin kasar nan ta manta da lamarinsa.


Al’umma da yawa na da labarai na kakanninsu wadanda suke amfani da darussansu. Domin fuskantar gaba misali Turawan Ingila na yawan tuba sadaukarwar sarki Henry. Jamusawa na tunawa da jarumtar Bobwisky. Yahudawa na tunawa da kisan gillar Masada. Dukkan wadannan tarihohi babu wanda ya yi armashi kamar sadaukarwa da kunar bakin wajen sultan Attahiru.


Darussan da ke cikin labarin nasa suna da yawa. Amma zan dauki biyu. Farko hijirarsa a takaice dakuma shahadarsa. Sai kuma muhawarar da aka yi tsakanin waziransa biyu a cikin littafin “THE STORY OF MAIMANA JEGA” Marubucin ya rubuta cewa lokacin da Turawa suka ga suna kame garuruwan Hausawa. Sai suka tura ‘yan rahotonsu domin yi masu bayanin shirye-shiryen sakkwato.


Shi kuma sultan Attahiru lokachin da ya samu tabbacin mamaya da cin yakin turawa a wasu daga garuruwan musulmi. Sai ya sanya waziransa biyu kowa ya kawo masa hujjar abin da ya kamata a yi a bisa hujjar Alqur’ani da Hadisi.


Waziri Alkadi Abdullah ya kawo hujja mai karfi ta ayi hijira a bar masu kasar, kamar yadda yazo a littafin “ULAMA AND COLONIALISM IN NIGERIA” Na Omar Bello. Shi kuma daya wazirin mai suna Bukhari ya kawo hujja ta cewa a yi sulhu da turawa kamar yacce yazo a littafin “THE DILEMMA OF WAZIRI” Na R.A Adekeye.


Hujjar a yi hijira ta rinjayi Sultan Attahiru. Amma bai matsawa duk wanda yake da wata hujja sa6anin wannan ba ya yi fatawar. “Kowanne ana masa hukunci a bisa a bin da yayi niyya” Bisa hujja da hadisin nan mai cewa “Duk aiki yana tare da niyya”.


Zanci gaba insha Allah……..


©️Imamu Mahadi Umar✍🏻

Post a Comment

0 Comments