Tarihin Gwagwarmayar sarkin Musulmi Attahiru I da Turawan Mulkin Mallaka kashi na ukwu.

Tarihin Gwagwarmayar sarkin Musulmi Attahiru I da Turawan Mulkin Mallaka kashi na ukwu.



Sojan Attahiru da suka rage bayan yakin sun fada cewa “mafi yawan wadanda suka isa Bormi babu wanda baida ciwo a jikinsa, wasu ma sun rasa wani 6angare na jikinsu a fadan da sukayi a hanya.


Kamar yacce na karanta sun isa garin daidai la’asar inda Sultan yayi umarni da ayi sallar azahar da la’asar, sannan a wajen bayan sallar Alkali Abdullahi ya tashi ya kara jaddada wannan matakin da suka dauka na sadaukarwa shine mafita kawai ya bayyana mahinmancin jihadi da shahada.


Ba’a gama jawabi ba turawa suka fara ruwan kibau inda a wajen suka kashe ladanin da yayi ladanci a lokacin, tun daga lokacin aka fara dauki ba dadi ana gwamzawa, da turawa sukaga Sultan ya tsaya yana sallah sai baki dayansu sukai mashi Zobe, suka tada baki daya kayyukan da suke kusa da garin.


Sannan suka bada Sanarwar Sultan ya mika Kansa cikin lalama. A nan ne ya sake maimaita masu sakon da ya sake aiko masu lokacin yana Sokkwato . “ Daga gare mu zuwa gare ku, ban gayyaci wani daga cikunku ya zauna damu ba, don haka ba zan ta6a yarda da ku ba. Babu wata alaqa a tsakaninmu dangantakarmu daku yaki na musulmi da kafirci, wanda Allah ya umarce mu mu yi.” Wannan sakon ya kara harzuka kwamandan dake tsare da sultan, sai ya aika da neman izini cewa, “ Sultan ba zai mika Kansa ba, Amman ina neman izini inyi anfani da karfin soja.” Ya kara da cewa “za mu iya lankwame su cikin awowi.” A daren kafin ansa tazo masa dakarun Suktan suka bi dare suka shiga dakarunsa suka masa muguwar 6arna.


6arnar da tayi sanadin karya lagon turawa, ance, ance wanda ya jagoranci wannan 6arna shine wanda ya kashe Bature ya kuma gudu yabi daji har ya hadu da rundunar Sultan ta Dan-yamusa na keffi. Turawa sun rubuta cewa Hassan Dan ya MUSA ya shirya wata kungiya ta yan ta kife daga cikin matasan dakarun Suktan (Yan taratsi 😆) wadanda suka tara bin dare suna shiga cikin dakarun Turawa suna aiki sosai.


Da kuma hawa bisa tsaunuka ko itatuwa suna ruwan kibau da harbo kifaffun itatu yana kashe sojan turawa. Da Gina rami ana dana tarko wanda ya dunga ma sojan turawa 6arna sosai. Duk da irin tsoratarwar da turawa suka ma kauyukan dake kewaye da Bormi saida suka rinka satar shiga da kayayyakin abinci zuwa ga dakarun Attahiru. Sojan sunyi iya kokarinsu suga sun kama garin Amman ya gagare su.


Sai da ta kai sojan turawa sun lura a yakin nan sune suke shan kasa, sai suka janye suka koma nesa da garin sukayi kokarin hana ruwa da abinchi isa ga dakarun Attahiru. Wannan ne ya azabtar da wannan Al’umma har takai da Sultan ya rubutawa kwamandan turawa cewa “kun rabo ni da gidana, kun tsare ni a nan, ku kyaleni mana in yi tafiya zuwa wata Qasa, a matsayin zanyi gudun hijira?”.


Amman sai Razdan ya aika masa da cewa, bazai kyale shi ya wuce ko’ina ba, saidai ya mika wuya kawai yayi saranda.


Zanci gaba insha Allah………….


©️Imamu Mahadi Umar✍🏻

Post a Comment

0 Comments