Turkiyya na fatan Amurka za ta cika alkawarin sayar mata da jiragen yakin F-16.

 Tattaunawar da ya yi da takwaransa na Amurka ta wayar tarho, Ministan harkokin wajen Turkiyya Fidan ya bukaci kasar ta cika alkawarin da ta yi na sayar musu da jiragen yaki samfurin F-16, kana ya jaddada bukatar tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza



 Turkiyya na fatan Washington za ta cika alkawuran da ta dauka na sayar da jiragen yaki samfurin F-16 ga Ankara, a cewar ministan harkokin wajen kasar Hakan Fidan yayin tattaunawa ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.


Ranar Laraba Fidan ya bayyana cewa Ankara tana fatan gwamnatin Amurka da Majalisar Dokokin kasar za su yi aiki bisa ga "karfin kawance da ke tsakaninmu wajen cika alkawuran da aka dauka,'' kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka rawaito.


Fidan ya kuma shaida wa Blinken cewa ana ci gaba da aikin tsare-tsaren tabbatar da Sweden a matsayin mamba a kungiyar tsaro ta NATO karkashin ikon majalisar dokokin Turkiyya.


Kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin Turkiyya ya amince da dokar, abin da ke nuna haske kan shigar kasar Sweden cikin kungiyar NATO a ranar Talata, inda a yanzu ake da kuri'a daya kacal da za a kada daga babban zauren majalisar wanda zai tabbatar ko kuma ya hana Turkiyya amincewa kan batun.


Hakan ya biyo bayan rattaba hannun shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan kan yarjejeniyar shigar Sweden kungiyar NATO a matsayin mamba tare da mika ta ga majalisar dokokin kasar a watan Oktoba.


Tsagaita wuta cikin gaggawa a yankin Gaza da aka yi wa kawanya


Fidan ta jaddada bukatar tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza da kuma fara tattaunawa kan hanyoyin samar da zaman lafiya.


Isra'ila ta kaddamar da wani gagarumin yaki na soji a yankin da aka yi wa kawanya bayan harin ba-zata da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba. Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 21,110, galibinsu mata ne da kananan yara, tare da jikkata mutane sama da 55,243, a cewar hukumomin lafiya na yankin.


Hare-haren sun matukar ruguza yankin Gaza, inda kashi 60 cikin dari na ababen more rayuwa a yankin suka lalace sannan kusan mutane miliyan 2 suka rasa matsugunansu, inda a halin da ake ciki suke fama da karancin abinci da tsaftataccen ruwan sha da magunguna.


Kimanin 'yan Isra'ila 1,200 ne ake kiyasi an kashe a harin da Hamas ta kai.


Kazalika, an kawo batun Cyprus a yayin tattaunawar ta wayar tarho.

Post a Comment

0 Comments