Turkiyya ta kama wanda ake kira shugaban gudanarwa kuma shugaban harkokin kudi na kungiyar Daesh

Jami'an leken asirin Turkiyya sun kama Huzeyfe Al Muri, da ake kira Eyyup, wanda ya yi aiki a Damascus na Siriya, a lokacin wani samame a kudancin Turkiyya.



Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya MIT ta kama wani dan ta'addar Daesh mai kula da bayar da tallafin kudi ga 'ya'yan kungiyar ta'addanci a yankunan da ake fama da rikici.


Ta hanyar binciken leken asirin da MIT ta yi, an kama wanda ake kira jami'in gudanarwa da harkokin kudi na ƙungiyar Daesh na lardin Damascus na kasar Siriya Huzeyfe al Muri, da aka fi sani da Eyyup, a wani samame da aka kai Mersin a ranar Talata bayan gano shi a farkon watan nan.


Sojojin na MIT sun kuma ƙwace dala 28,800, da Yuro 14,950, da kuma Lira 31,800 na Turkiyya a lokacin samamen, tare da wasu kayan dijital na kungiyar.


An kuma gano wasu ayyuka da aka aiwatar da waya da abubuwan da Daesh ke amfani da su wajen aika kudi kuma jami’an leƙen asiri sun fara tantance mambobin kungiyar.


Turkiyya dai na ci gaba da yaƙar ta'addanci a ƙasar Siriya da ma sauran yankuna, inda ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da nuna bambanci tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda irinsu Daesh ko Al Qaeda ko PKK ba.

Post a Comment

0 Comments