An haife Shi a cikin garin Gaya ta jihar Kano a shekarar 1950. Ya haddace Alqur’ani yana da shekara 11, ya gama duk wani fanni na ilimi da ake karantawa a makarantun soro (karshen ilimi kenan a wancan lokacin) yana da shekaru 15. Ya fara rubutun Alkur’ani yana da shekaru 13, ya zama Alaramma mai darasu tun yana da shekaru 14.Tsangayata tana nan a halin yanzu a Gashua, a Katuzu/Garin Yamma, jihar Yobe. Mallam Musa Dan Dikkware shi ne Halifan Shi mai darasu a halin yanzu. Ya fara shimfiɗa buzu na karantar da dalibai a makarantar soro tun daga Gashua Katuzu, har zuwa Kano a gida mai lamba 32 Chiranci.
Malamanshi sun hada da Mahaifinshi da Mallam Ali Ɗan Gunka, da Sheikh Muhammadu Arabi, duk a Gaya. A Jihar Borno da Yobe, ya zauna a duk wata Tsangaya da ta yi suna da tashe a wancan lokaci; kamar Girgir, Jakusko, Alagarno, Jaba, Badigana, Bindigi, Jajere, Nangere, Kolere, Koriyal, Abbari da sauransu. Saboda haka bai san iyakar malaman sa ba, sai dai kamar Mallam Haruna Mai Dogon Gemu, da Sheikh Muhammadu Jinjiri, a Gashua, amma a Kano Sheikh Uthman Qalansawy ( Shehu Maihula) ne Malamin sa kuma Shehinsa. Har yanzu fa bai shiga Sakandare ba, kuma bai yi aure ba. Ya ci gaba da karantar da Alqur’ani da ilimai, da budewa da gudanar da makarantun Islamiyya, da rubuta Alqura’anai har 1971.
Daga 1971, nan ya bude wani sabon shafi na rayuwa ta ilimi, inda ya shiga makarantar sakandire ta School For Arabic Studies, SAS da ke Kano. Ya gama a shekarar 1974. Yayi Diploma a jami’ar Ahmadu Bello a Zaria,ya yi degree na daya, da na biyu da na uku a jami’ar Bayero a Kano. Ya kuma samu kyautar girmamawa na dakta daga jami’ar Albart, kasar Canada. Ya yi bautar ƙasa a shekarar 1982. Bayan haka kuma ya halarci kwasa-kwasai da dama da tarurruka na kara wa juna ilimi, ciki da wajen Nigeria.
Shehin malamin ya rasu ne a ranar 6 ga watan nuwamba na shekarar Dubu biyu da ashirin da ukwu anyi jana'izar sa a Masallachin Murtala da ke kan titin Gidan Zoo.
Allah ya jikan malam.
0 Comments