Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 16 tare da jikkatawa da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

 Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 16 tare da jikkatawa su 17 a jihar Kaduna.



Rahotonni Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 16 tare da jikkatawa da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja.


sunun ambato kwadandan Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Najeriya mai lura da jihar Kabir Nadabo na cewa hatsarin ya auku ne a ƙauyen Audu Jhangon da ke kan babban titin Abuja zuwa Kaduna


Ya ce hatsarin ya auku ne da asubahin ranar Lahadi lokacin da wata babar motar daf, ta ƙwace wa direbanta tare da faɗa cikin rami.


“Rahotonnin farko da muka samu sun nuna cewa direban na tsakiyar gudun wuce kima'', in ji Nadabo.


Ya ce tuni jami'an hukuar suka kai ɗauki domin tseratar da mutanen da lamarin ya shafa.


“Hatsarin ya rutsa da mutum 65, inda mutum 27 suka jikkata, yayin da 16 suka mutu''.


Ya ce tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibiti domin ba su kulawar gaggawa.


Hatsarin mota dai wata babbar matsala ce a titunan Najeriya, da ke laƙume rayukan 'yan ƙasar masu yawan gaske a kowace shekara.


Matsalar da masana ke alaƙantawa da rashin kyawun titunan ƙasar, da kuma rashin bin ƙa'idojin tuki daga ɓangaren direbobi.

Post a Comment

0 Comments