Yacce aka kama ƴan sandan da suka roƙi baturiya kuɗi

 


Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Juma’a ta ce ta kama wasu ‘yan sandan sa-kai wadanda aka gani a wani faifan bidiyo suna roƙon kudi daga hannun wata mata ‘yar ƙasar Holland mai tuka babur a unguwar Ojongbodu da ke kan titin Iseyin/Ogbomosho a jihar Oyo.


Bayanin kama su ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Muyiwa Adejobi, ya fitar, inda ya ce an kama su ne saboda rashin ɗa’a, wanda ba za a amince da shi ba, da kuma hukunta su.


Adejobi ya kuma bayyana cewa "Kwamishanan 'yan sanda na jihar Oyo, CP Adebola Ayinde Hamzat, ya ƙaddamar da binciken ladabtarwa kan lamarin nan take."


“Hukumar ‘yan sanda ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da bayar da umarnin hukunta ‘yan sandan sa-kan da jami’in ‘yan sanda da ke sa ido a kan su.”


Ya bayyana lamarin a matsayin wanda ya ci karo da ɗabi'ar ‘yan sanda ba kuma ba za a taba amincewa da shi ta kowace hanya ba.

Post a Comment

0 Comments