Yacce aka kashe Sarkin Musulmi Attahiru, Karshen Tarihin Gwagwarmayar Sarkin Musulmi Attahiru I Da Turawan Mulkin Mallaka.
A sati na uku ne da yi wa Sultan kawanya ana kallon hadarin kaji sun ki kai masu hari, amma suna kewaye da su, sun datse duk wani taimakon ruwa da abinci isa gare su.
Sai kwamandan rundunar sojan turawa ya aika da cewa sojan da yake tare dashi basu iyawa da dakarun sultan. Don haka domin su samu nasara a wannan yakin yana neman gudummuwar soja, an aiko mashi da cewa kamar soja nawa yake so?
Sai yace “Ina son gwanaye kuma gogaggu, sannan masu yawan gaske, domin fadan na yi ne da makamai manya-manya”. Taron gudummuwar sojan turawa sun isa Bormi a 26yuli, suka sauka a kudancin kasar. Sun iso ne daga kasashen Ghana, lokachin ana kiran ta Gold Coast, Saliyo da garin Legas.
Sultan Attahiru ya kalli lokacin da ake sauke sojan ta hasumiyar masallacin Bormi, suna tare da wazirinsa Alkali Abdullahi, sultan ya dubi wazirinsa yace “lamarin ya kai inda ya kai” wazirin yace “ya Amir babu wani tantama yau a daren nan zamuyi barci ne a gidan Aljanna.” Duk da wannan taron dangin da kayan fada na fin karfi da turawa suka tattaro, wannan bai sa ya karaya ba . Shine wanda ya tara rundunarsa kuma ya fara kai farmaki ga sojin turawa.
Turawa sun rubuta cewa sun ga fada na jarumta a wannan rana, fadan da basu ta6a ganin irinsa ba. An fara gumurzu 11:30 na safe, amma har dare turawa ba su debi na miya daga dakarun Attahiru ba. Da dare yayi suka canza salo, inda suka janye dakarunsu suka mirgino wasu manya-manyan iyawa wadanda suka zo dasu. Sannan suka hada da ruwan nakiyoyi manya Manya sannan suka hada da ruwan harsasai babu kakkautawa ta haka suka ragargaza masallacin da Attahiru yake ciki.
Dayake a daidai lokacin Attahiru yana waje ana cikin wannan yanayin ne wani Alburushi ya sami sultan Attahiru akai ta wajen goshi, daman tun kafin lokachin an kshe wazirinsa Alkali Abdullah.
Sultan na faduwa kasa akai wata kuwa “an kashe sarkin muminai” don da dakarun musulmai sukai wani kukan kura suka tarwatsa sojan turawa suka tarwatse. Muhammad Bello mai wurno dan Attahiru yayi gabas shida wasu har saida ya dangane da kogin Nilu, can cikin Sudan kusa da wani Shahrarren malami, Sheikh Talla. Nan jama’an Sudan suka bashi wajen zama ya kafa gari wanda har yanzu yanann ana kiran garin da Maiwurmo.
©️Imamu Mahadi Umar✍🏻
0 Comments