Yan sanda sun harbe Pablo Escobar mai safarar kwaya dan Colombia a Medellín.

 Yan sanda sun harbe Pablo Escobar mai safarar kwaya dan Colombia a Medellín.


A Rana Mai Kamar Ta Yau Ga 2 Ga Watan Disamba 1993 ‘ Yan sanda suka harbe Pablo Escobar mai safarar kwaya dan Colombia a Medellín.



A ranar 1 ga Disamba, 1993, Escobar bayan ya yi bikin cika shekaru 44 da haihuwa. Washegari aka gano maboyarsa a Medellín. Yayin da sojojin da Yansandan Colombia suka kutsa kai cikin ginin da Escobar da wani mai gadi suke. An yi ta fafatawa da bindiga, kuma daga karshe an harbe Escobar, ya mutu har lahira. 


Pablo Escobar dan kasar Colombia ne kuma mai fataucin miyagun kwayoyi, wanda galibi ake kira da "Sarkin Cocaine"


Cikakken sunansa Pablo Emilio Escobar Gaviria.


An haife shi a ranar 1 ga Disamba, 1949, a Rionegro, a Sashen Antioquia na kasar Colombia ya rasu a ranar 2 ga Disamba, 1993.


A lokacin da ya fara aikin safarar miyagun kwayoyi, yana ba da kimanin kashi 80 cikin 100 na hodar Iblis da ake shigo da su Amurka, inda ya ke juya sama da dala miliyan 60 a rana, ko dala biliyan 21.9 a shekara.


Shi ne wanda ya fi kowa arziki a tarihin safarar kwaya, in da aka kiyasta kudinsa ya kai dalar Amurka biliyan 30 a farkon shekarun 1990.


Ya kuma kasance daya daga cikin attajirai 10 a duniya a lokacinsa kuma ya zauna a cikin Kasaitaccen Gidan Gona na (Hacienda Nápoles) Wanda da ya gina da kansa.


Shi ne na uku cikin Ya'ya bakwai na mahaifinsa Abel de Jesús Dari Escobar wanda manomi ne, da mahaifiyarsa Hermilda Gaviria, wata malamar makarantar firamare.


Tun yana matashi a kan titunan Medellín, ana kyautata zaton ya fara aikata laifuka ne ta hanyar satar duwatsun kaburbura da yashi domin sake sayar da su ga masu fasa-kwauri.


Dan uwansa kuma kawunsa, Roberto Escobar, ya musanta hakan, yana mai da’awar cewa dutsen kaburbura yana fitowa ne daga masu makabartu wadanda abokan huldarsu suka daina biyan kudin kula da wurin kuma suna da wani dan uwa da ke kasuwancin tunawa da mamata.


Pablo Escobar yayi karatu na dan kankanin lokaci a Universidad Autónoma Latino americana ta Medellín, amma ya bar jami'a ba tare daya gama digiri ba.


A ƙarshe Pablo Escobar ya shiga cikin ayyukan laifuka da yawa tare da Oscar Benel Aguirre - yana gudanar da zamba a kan tituna, sayar da sigari da tikitin caca na jabu, da satar motoci.


A farkon shekarun 1970, ya kasance barawo kuma mai gadi, kuma ana zarginsa da samun $100,000 ta hanyar sacewa da kabar kudin fansa, kafin ya shiga kasuwancin miyagun ƙwayoyi.


Mataki na gaba da ya taka shi ne ya zama miloniya ta yin aiki da Alvaro Prieto wani shahararren mai fasa kwauri. 


Burin Pablo Escobar tun yana yaro shi ne ya samu kudi miliyan na peso (kudin kasar Mexico) a lokacin yana dan shekara 22.


A lokacin yana dan shekara 26, Pablo Escobar ya ajiye peso miliyan 100 (fiye da dalar Amurka miliyan 3) a bankin Colombia.


A watan Maris na shekara ta 1976, sa’ad da yake ɗan shekara 27, Pablo Escobar ya auri Maria Victoria, wadda a lokacin tana ’yar shekara 15.


A shekara ta 1975, Pablo ya fara haɓaka sana'ar cocaine. musamman tsakanin Colombia da Panama, ta hanyar fasa kwauri zuwa Amurka.


A lokacin da ya sayi sabbin jiragen sama guda 15 da manya da suka hada da Learjet da jirage masu saukar ungulu shida.


Ba da dadewa ba, buƙatun hodar iblis ya ƙaru a Amurka, kuma Escobar ya shirya ƙarin jigilar kayayyaki, da hanyoyin rarrabawa a Kudancin Florida, California, da sauran sassan ƙasar. Shi da wanda ya kafa Cartel Carlos Lehder sun yi aiki tare don haɓaka sabon wurin jigilar kayayyaki a cikin Bahamas a tsibiri da ake kira Norman's Cay kusan mil 220 (kilomita 350) kudu maso gabas na gabar tekun Florida.


Ba da daɗewa ba Escobar ya sami damar siyan fili mai faɗin murabba'in mil 7.7 (kilomita 20) a Antioquia akan miliyoyin daloli wanda a kai ya gina Gidan Gonarsa na Hacienda Napoles.


A wani lokaci, an kiyasta cewa 70 zuwa 80 ton na hodar iblis ana jigilar su daga Colombia zuwa Amurka kowane wata.


A tsakiyar Shekarar 1980 Escobar's Medellín Cartel yana jigilar kaya kamar ton 11 a kowace jirgi a cikin jiragen sama zuwa Amurka.


Roberto Escobar ya kuma yi iƙirarin cewa, baya ga amfani da jiragen sama, ɗan'uwansa ya na amfani da ƙananan jiragen ruwa guda biyu don ɗaukar manyan lodi.


A 1982, Escobar aka zaba a matsayin memba na Chamber of Representative of Colombia, a matsayin wani ɓangare na Colombian Liberal Party.


Escobar cikin sauri ya zama sananne a duniya kamar yadda yake shigar da miyagun kwayoyi Amurka, Mexico, Puerto Rico, Jamhuriyar Dominican, Venezuela, da Spain, har aka yi jita-jitar ya na kai wa har zuwa nahiyar Asiya.


Yan bangarsa sunyi Kisa wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da suka hada da farar hula, 'yan sanda, da jami'an gwamnati.


Ana zarginsa da alhakin kisan dan takarar shugaban kasar Colombia Luis Carlos Galán a shekarar 1989, daya daga cikin 'yan takara uku da aka kashe a lokacin zaben 1990.


Har ila yau, shi ne ke da alhakin tashin bam a jirgin Avianca Flight 203 a shekarar 1989 da kuma DAS Building a birnin Bogotá na kasar Colombia. 


Pablo Escobar ya ce kasuwancin hodar Iblis Abu ne mai sauƙi: ka ba wa wani cin hanci a nan, ka ba wa wani cin hanci a can, kuma kayi abokantaka da ma’aikacin banki ka biyashi don ya taimake ka, ka kwashe kuɗin ka.


A shekara ta 1989, mujallar Forbes ta kiyasta Escobar na ɗaya daga cikin attajirai 227 a duniya da ke da kuɗin da ya kai kusan dalar Amurka biliyan uku.


A wajen Talakawa jarumi sosai, ya kasance mai iya hulda da jama'a, kuma ya yi aiki don samar da kyakkyawar fata a tsakanin talakawan Colombia.


Pablo Escobar ya gina asibitoci da makarantu da majami'u da dama a yammacin Colombia, wanda hakan ya sa ya shahara a cikin Cocin Roman Katolika na kasar.


Ya yi aiki tuƙuru don rarraba kuɗi ta hanyar ayyukan gidaje da sauran ayyukan jama'a, wanda ya sa ya shahara a cikin talakawa.


​​Kwanan Pablo Escobar ya ƙare a ranar 2 ga Disamba 1993, a cikin wani yunƙurin Escobar na kubuta daga masu Bincike.


A zahiri ba a tabbatar da wanda ya harbe a kai ba, ko kuma tantance ko an yi wannan harbin ne a lokacin batakashin da akayi dashi, ana ta cece-kuce game da batun.


Wasu daga cikin dangin Escobar sun gaskata cewa zai iya kashe kansa.


Jama’a da yawa sun yi ta jimamin mutuwarsa, musamman talakawan birnin da Escobar ya taimakawa tun yana raye. Kimanin mutane 25,000 ne suka halarci jana'izar sa.

Post a Comment

0 Comments