Yan ta’adda suna samun mafaka a makarantu a Barkin-Ladi tsawon shekaru — Gwamnan Filato.

‘Yan ta’adda suna samun mafaka a makarantu a Barkin-Ladi tsawon shekaru — Gwamnan Filato.

Gwamnan, wanda ya fadi hakan a cikin shirin gidan talabijin na Channels, Sunrise Daily , ya ce rikice-rikicen da ake fama da su a jiharsa na ta’azzara ne saboda jami’an tsaro ba sa yin wani kame kan lamarin.




 Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang ya koka kan cewa ƴan ta’adda sun shafe shekara biyar suna mamaye makarantu a ƙaramar hukumar Barkin-Ladi ba tare da an tarwatsa su ba.


Gwamnan, wanda ya fadi hakan a cikin shirin gidan talabijin na Channels, Sunrise Daily , ya ce rikice-rikicen da ake fama da su a jiharsa na ta’azzara ne saboda jami’an tsaro ba sa yin wani kame kan lamarin.


“Daga cikin abin da ke rura wutar matsalar har da rashin yin kame ko gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu, don haka mutane na ganin kamar ana bai wa maharan kariya ne,” ya ce.


Waɗannan kalamai na Gwamna Mutfwang na zuwa ne a lokacin da aka kai wasu hare-hare kan wasu ƙauyuka da suka yi sanadin mutuwar sama da mutum 140 a ƙarshen mako, lamarin da ya tayar da hankalin al’ummar jihar.


Har yanzu ba a san waɗanda suka kai harin ba, sai dai hare-haren ƙabilanci da na rikicin makiyaya da manoma sun zama ruwan dare a jihar ta Filato.


Cikin takaici, gwamnan ya koka kan wannan sabon hari da aka kai, wanda bayan asarar rayukan da aka yi, ya kuma yi sanadin jikkatar ɗaruruwan mutane da ƙona gidaje a ƙananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi.


A hirar tasa ta Channels TV, gwamnan ya kuma soki gwamnatin tarayyar Nijeriya kan abin da ya kira “rashin son ɗaukar mataki” na kawar da ƴan ta’addar da ke cin karensu babu babbaka a jihar.


“Maganar da nake yi a yanzu, ƴan ta’adda sun mamaye makarantun ƙaramar hukumar Barkin-Ladi tsawon shekaru. An tarwatsa aƙalla al’ummomi 64 sannan waɗannan ƴan ta’addan da ke cin karensu babu babbaka sun ƙwace yankunan,” in ji gwamnan.


Gwamnan na Filato ya ce zai tuntuɓi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu don ya bai wa jami’an tsaro umarni ƙarara na kare al’ummar Filato daga maharan da ke ƙwace musu wuraren zama.


“Zan yi magana da Shugaban Ƙasa a kan wannna batun. Muna buƙatar mu samu ƙwarin gwiwar bai wa hukumomin tsaro umarnin kare mutuncin Nijeriya da ma kare yankunanmu.


“Dole mu dakatar da wannan masifar, kuma bai kamata jami’an tsaro su ci gaba da bin matakan da suke ɗauka a yanzu ba, dole su ƙara ƙaimi,” a cewar gwamnan.

Post a Comment

0 Comments