YAN UWA MUSULMI ALMAJIRAN SHEIKH ZAKZAKY SUN GUDANAR DA ZANGA-ZANGAR LUMANA DON ALLAH-WADAI DA TA'ADDANCIN SOJOJIN NIJERIYA KAN MASU MAULIDI A JAHAR KADUNA.

 YAN UWA MUSULMI ALMAJIRAN SHEIKH ZAKZAKY SUN GUDANAR DA ZANGA-ZANGAR LUMANA DON  ALLAH-WADAI DA TA'ADDANCIN  SOJOJIN NIJERIYA KAN MASU MAULIDI A JAHAR KADUNA.



Muzaharar wacce almajiran shehin malamin suka duganar a babban birnin Tarayyar Nijeriya Dake Abuja.

Harkar Musulunci Karkashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), ta gudanar muzaharar Allah-wadai da ta'addancin da Sojojin Nijeriya sukayi na jefawa masu Maulidi bom ta jirgin sama, Wanda hakan yayi Sanadiyar rasuwar mutane sama da 200, maza da Mata, yara da manya.


A gefe guda kuma yan'uwan kamar yadda suka Saba, suna dauke da tutoci da fostoci na ta'addancin kasar Israel ga al'ummar Palestine, suna bayyana goyon bayansu ga al'ummar Palestine tare da yin Allah wadai da ta'addancin Haramtattun kasashen Israel da American, Kan Palestine.


Muzaharar wacce ta gudana tun daga bakin Masallacin Annurr har zuwa Junction na Shiga Masallacin, a Wuse !! Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja.


Isa Charis ✍️

Ibraheem A'immah

8th December 2023

Post a Comment

0 Comments