YANZU-YANZU: HUKUMAR KARE HAKKIN ƊAN ADAM TA KARƁI TAKARDAR KORAFI AKAN KISAN MUSULMI A TUDUN MAULIDI (BIRI)

YANZU-YANZU: HUKUMAR KARE HAKKIN ƊAN ADAM TA KARƁI TAKARDAR KORAFI AKAN KISAN MUSULMI A TUDUN MAULIDI (BIRI) 

Harkar Musulunci ta gabatar da takardar kira ga hukumar kare hakkin ɗan Adam kan kisan kiyashin da sojoji sukayi kan musulmi masu maulidi a Tudun Maulidi (Biri) Ijabi Kaduna.

A yau Litinin, ƴan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) suka sake fitowa muzaharar Allah wadai da kisan kiyashin da sojojin Najeriya sukayi kan masu maulidi a Tudun Maulidi (Biri) Igabi Kaduna, muzaharar wacce ta gudana a unguwar Maitama layin Human Rights.

Da misalin karfe Biyu da Ashirin, yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) suka fito kan titin Aguiyi Ironsi dake unguwar Maitama, dauke da babban hoto dake dauke da irin ta'addanci sojoji da sukayi a harin da suka kai kan masu maulidi a Tudun Maulidi Kaduna.

Haka muzaharar ta ci gaba da tafiya daga gidan man AP har zuwa junshon na NCC, daga nan ta juya har zuwa gaban ofishin hukumar kare hakkin dan adam wato (Human Rights Commission) Abuja, wanda anan aka gabatar da gangami har wakilai daga ma'aikata suka fito.

Engineer Abdullahi Musa ya gabatar da takardar da ake tafe da ita, takardar wacce take dauke da kira ga hukumar ta kare hakkin ɗan Adam da tayi aikinta wurin kira ga shugaban kasa da a tabbatar da a hukunta wanda sukayi wannan ta'addanci, da kuma biyan diya ga iyalan wanda aka kashe.

Ga kadan daga cikin hotunan muzaharar da gangamin na yau Litinin.

-Asperger
11-12-2023

Post a Comment

0 Comments