Za a daɗe ana yaƙin Gaza, ba za a gama nan kusa ba: Netanyahu

 Za a daɗe ana yaƙin Gaza, ba za a gama nan kusa ba: Netanyahu



Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yaƙin da ake gwabzawa a Gaza bai kai ga kawo ƙarshe ba, ya kuma yi watsi da abin da ya kira a matsayin raɗe-raɗin ƙarya da kafafen yada labarai ke yadawa cewa gwamnatinsa na iya dakatar da yaƙi da Hamas.


“Ba za mu tsaya ba, muna ci gaba da fafatawa, kuma za mu ƙara tsananta fadan a cikin kwanaki masu zuwa, kuma za a dauki tsawon lokaci ana gwabzawa, kuma ba a kusa aamawa ba,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar daga jam’iyyarsa ta Likud, a cewar wani dan majalisar a wata sanarwa.


 — Karancin kayan kula da lafiya a Gaza ya laƙume rayukan dubban Falasdinawa


Akalla mutum 9,000 ne suka mutu a Gaza sakamakon rashin kayayyakin aikin asibiti a yayin da Isra'ila ke kai wa hari, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnati ya bayyana.


Mutum 250 aka kashe a Gaza cikin awa 24 — Ma'aikatar Lafiya


Akalla Falasdinawa 250 ne suka mutu yayin da wasu 500 suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu ya kai 20,674 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta yi wa ƙawanya.


Ma'aikatar ta kuma ƙara da cewa mutane 54,536 ne suka samu raunuka tun bayan fara yakin Isra'ila a yankin.

Post a Comment

0 Comments