Abubuwa 18 da aka haramta a yayin aure a jihar kano ciki harda yin lefe.

 Abubuwa 18 da aka haramta a yayin aure a jihar kano ciki harda yin lefe.



Shahararren lauyan nan na jihar kano Mai rajin kare hakkin al'umma ya bankado wasu dokoki Wanda idan mutum ya sa6asu zai iya yin gidan yari na wata biyu kokuma ya biya Tara.


Dalilin yin wadannan dokokin dai shine don ganin an samu sauki a wajen yin aure dakuma  inganta lamarin auren.


An yanke hukuncin Zaman gidan yari na wata biyu ga duk Wanda ya sa6a wadannan dokokin.


Dokokin gasunan kamar haka 👇

1. Gaisuwar uwa da uba laifi ne

2. Kudin zance da kayan zance.

3. Kayan lefe laifi ne duk Wanda yayisu kokuma Wanda ya kar6a ko Wanda ya taimaka akayi wata biyu a gidan yari.

4. kayan baiko laifi ne.

5. Kayan Ada'a

6. Kudin aure 

7. Kudin rigar Mijin baya

8. Kudin budar kai

9. Kudin Yan Mata

10. Kudin alugudi

11. Sayen fura

12. Zaman Ajo

13. Sayen Baki 

14. Kudin kama hannu

15. Garar aure da garar haihuwa

16. Yinin Biki.


Wadannan sune dokokin duk Wanda ya karyasu akwai hukunci Mai tsanani.

Yan sanda sunada damar kama duk Wanda ya aikata wadannan laifukan domin kuwa a tsarin Hukuma Yan sandan Najeriya ta Bada damar Dan sanda zai iya kama wanda ya sa6a dokokin jiha ko na karamar hukuma.


Kuma wani zai iya shigar da Kara muddin yaga an aikata wannan laifin a jihar kano.


® Mahadi Umar Imam ✍️

Post a Comment

0 Comments