Akalla mutane Sama da 100 suka Rasa rayukansu a harin bam din da aka kai yau kusa da kabarin kwamandan sojojin Iran Qasem Soleimani wajen bikin Tunawa da shahadarsa.

 Akalla mutane Sama da  100 suka Rasa rayukansu a harin bam din da aka kai yau kusa da kabarin kwamandan sojojin Iran Qasem Soleimani wajen bikin Tunawa da shahadarsa.



Kafin kasar Amurka ta kashe Soleimani Yana daya daga cikin manyan mutanen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Soleimani shi ne shugaban dakarun Quds Forces na Juyin Juya Hali, wani sashe na musamman ne da ke kula da ayyukan Iran a ketare. 


Ma'aikatar tsaron Amurka ta pentagon ta ce Soleimani da sojojinsa suna da alhakin Mutuwar daruruwan Amurkawa da sojojin kawance da Kuma jikkata wasu dubbai. 


Wanda aka fi sani da kwamandan inuwar Iran, "Soleimani Wanda ya jagoranci rundunar Quds tun 1998, shi ne Jagoran ayyukan sojojin Iran a Iraki da Siriya.


Fashewar bam din ta zo a cikin tashin hankali a yankin fashewar ta faru ne a daidai lokacin da ake Kara samun tashin hankali a yankin a daidai lokacin da Isra'ila ke yaki na tsawon watanni uku da Hamas a Gaza a sakamakon harin da Isra'ila take kaiwa a zirin Gaza.


Wannan yakin yayi sanadiyar mutuwar mutune fiye da 23,000 a Gaza, Hakan ya haifar da fadace-fadace Wanda galibi ya hada da mayakan da kai da Iran ke marawa baya.


A ranar Talata an kashe Wani babban shugaban Hamas a wata unguwa da ke birnin Beirut a wani harin bam da Wani Jami'in Amurka ya shaida mana Isra'ila ce ta Kai shi. Hamas da kungiyar Hizbullah, wacce ke iko da yankin sun zargi Isra'ila Kuma sun sha alwashin daukar fansa.


Har zuwa hada wannan rahoton bamuda cikakken masaniya akan wadanda suka jagoranci Kai wannan harin amman ana anfi zargin kasar Isra'ila da Amurka da hannu wajen Kai wannan harin kunar bakin waken Wanda yayi sanadin rasa rayukan mutum Sama da 73.


Ku kasance da muryar Labarai domin kawo maku yacce lamarin ya kasance.

Post a Comment

0 Comments