Al'amarin Falasɗinu shi ne kan gaba, al'amari ne da ya fi damun mu. - Sheikh Zakzaky..

 “Al'amarin Falasɗinu shi ne kan gaba, al'amari ne da ya fi damun mu. 



Masu kai hare-hare suna kashe Falasɗinawa in da za su samu dama za su kashe dukkan Musulmi. Ba kawai su makiyan ƴan adamtaka bane, su na hankoron kafa wani tsari ne na daban a ƙarƙashin kulawarsu. Su kuwa Falasɗinu da suke gwagwarmaya su na yi don al'ummar duniya da ake zalunta, ba don amfanin kansu kawai suke yi ba, suna wakiltar dukkan Musulmi ne, da dukkan wani mutum mai hankali.


“Su masu kisa, in da za su samu damar ƙarar da duk Musulmi (wanda hakan ba zai yiwu ba), to da za su yi hankoron gamawa da sauran mutane ne (bakidaya). Al'amarin Falasɗinu yana hada kanmu ne gabaɗaya, babu wata al'umma da ta ke shan wahala kwatankwacin yadda Falasɗinawa suke shan wahala, sannan ka kalli yadda suka jure suka dake, wanda hakan ya zama darasi ga sauran al'ummomin da ake zalunta a duniya. A bayyane yake cewa ba suna yaƙi bane don karan kansu, suna yin yaƙi a madadinmu ne gabaɗaya.” 

Wani bangare na firar sheikh Ibraheem Zakzaky a hirarsa da PressTV ranar 9/1/2024. 


@Szakzakyoffice 

#GazaGenocide

#PrayForPalestine 

11/01/2024

Post a Comment

0 Comments