An kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Abuja

An kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Abuja



A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce rundunar ƴan sanda ta Jihar Kaduna ce ta yi nasarar kama wanda ake zargi da satar mutanen ranar Alhamis 18 ga watan Janairun 2024.


Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta Abuja ta ce an yi nasarar kama wani da ake zargin gawurtaccen mai yin garkuwa da mutane ne a babban birnin kasar mai suna Chinaza Phillip.


A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce rundunar ƴan sanda ta Jihar Kaduna ce ta yi nasarar kama mai satar mutanen ranar Alhamis 18 ga watan Janairun 2024.


"Daga nan sai rundunar ta Kaduna ta miƙa shi ga rundunar ƴan sanda ta Abuja a yau Juma'a 19 ga watan Janairun 2024, kuma a yanzu haka yana hannun ƴan sanda," in ji sanarwar.


Rundunar ƴan sandan ta ce za ta yi ƙarin bayani a nan gaba kaɗan, sai dai ta wallafa hoton Chinaza da kuma na wasu bindigogi da ba ta yi bayani a kansu ba.


Wannan babban kame yana zuwa ne a lokacin da ake ta samun ƙorafe-ƙorafe da koke-koke a kan yawan satar mutane don karɓar kudin fansa da ake yi a Abujan, ciki har da na wasu ƴan mata shida ƴan gida ɗaya da ya ɗaga hankalin al'ummar ƙasar.


Daga baya masu garkuwa da mutanen sun kashe babbar cikin yan matan mai suna Nabeeha, waɗanda aka sace su a gidansu da ke garin Bwari da ke ƙarkashin birnin tarayyar.


Kwanaki kaɗan bayan sace Nabeeha da ƴan'uwanta kuma an yi ta samun labarai na satar mutane duka a babban birnin.


A ranar Larabar da ta gabata ma rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ƙaddamar da wata runduna ta musamman mai suna SIS domin yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a fadin kasar, musamman a babban birnin tarayya, Abuja.


Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun wanda ya kaddamar da rundunar ya ce ta ƙunshi ƙwararrun jami’an ‘yan sanda na musamman, da ingantattun kayan aiki da kuma na’urorin tafi da gidanka.


Ya kuma ce rundunar na da ƙarfin shiga tsakani da gaggawa da kuma daƙile munanan matsalolin tsaro, kamar wadanda a halin yanzu ke barazana ga jami’an tsaro a kewayen birnin tarayya da kuma haifar da firgici gaba ɗaya.

Post a Comment

0 Comments