An kubutar da 'yan'uwan Nabeeha daga masu garkuwa da mutane

 An kubutar da 'yan'uwan Nabeeha daga masu garkuwa da mutane



Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja Josephine Adeh ta ce an kubutar da ‘yan matan 'yan'uwan Nabeeha ne a kusa da dajin Kajuru da ke Kaduna ranar Asabar da misalin karfe 11:30 na dare.


Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce jami'an tsaro sun kubutar da 'yan matan nan biyar da ke hannun masu garkuwa da mutane bayan 'yan bindiga sun kashe 'yar'uwarsu wato Nabeeha Al-Kadriyar.


An sace 'yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki a gidansu da ke Bwari a Abuja.


Sai dai daga bisani 'yan bindigar sun saki mahaifinsu sannan suka bukaci ya nemo N60m a matsayin kudin fansa.

Lamarin ya dauki sabon salo bayan 'yan bindiga sun kashe Nabeeha a yayin da wata makusanciyarsu Asiya Adamu take tattara kudin fansar bayan ta roki mutane a shafukan sada zumunta.

Post a Comment

0 Comments