An saki Oscar Pistorius na Afirka ta Kudu daga gidan yari

 An saki Oscar Pistorius na Afirka ta Kudu daga gidan yari

An saki Pistorius a ranar Juma'a ne bayan ya shafe kusan shekaru 11 a gidan yari sakamakon samunsa da laifin harbe budurwarsa Reeva Steenkamp.



An saki tsohon shahararren dan wasan tseren nakasassu na Afirka ta Kudu Oscar Pistorius daga gidan yari a ranarJuma’a, bayan ya shafe kusan shekaru 11 a tsare bisa laifin harbe budurwarsa Reeva Steenkamp, labarin da ya mamaye duniya.


Sashen hukumar gyaran hali na Afirka ta Kudu ya tabbatar da sakinsa da safiyar ranar Juma'a yana mai cewa a halin yanzu "yana gida."


Bayan ya shafe fiye da rabin hukuncin da aka yanke masa, dan wasan mai shekaru 37 da ya rasa kafafunsa biyu, ya bar gidan yarin Atteridgeville da ke wajen babban birnin kasar Pretoria.


Pistorius ya shahara kuma an fi saninsa da "Blade Runner" a duniya saboda yadda aka kera kafafun karfen da ya ke amfani da su.


Daga cikin sharadin sakinsa ba shi da 'yancin yi magana da kafafen yada labarai.


Neman Afuwa da dama


Hukumomin gidan yarin sun gargadi manema labarai cewa ba za a basu wata dama ta daukar shi hoto ba.


Pistorius ya kashe budurwarsa Steenkamp, sarauniyar kyau mai shekara 29 a lokacin, da safiyar ranar masoya ta Valentine a shekarar 2013, inda ya yi harbi har sau hudu ta kofar bandakin gidansa da ke Pretoria.


Harbin ya biyo bayan shekara guda da Pistorius ya kafa tarihi inda ya zama dan wasa na farko da ya lashe gasar Olympics a lokacin da ya fafata da wasannin da aka yi a London a shekarar 2012.


An same shi da laifin kisan-kai kuma an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 13 a shekarar 2017 bayan dogon lokaci da aka kwashe ana shari’a da daukaka kara.


Ya musanta aikata laifin da kuma musanta kashe Steenkamp, yana mai cewa ya yi zaton wani mahari ne ya yi kokarin shigo masa gida.


Mahaifiyar Steenkamp ta ce ba ta yarda cewa ya fadi gaskiya kan abin da ya faru ba.

Post a Comment

0 Comments