An tura tsohon Ministan Lantarki gidan yarin Kuje kan badakalar kwangilar Mambila

 An tura tsohon Ministan Lantarki gidan yarin Kuje kan badakalar kwangilar Mambila.

A watan Disamba hukumar EFCC ta ayyana tsohon ministan a matsayin wanda take nema ruwa-a-jallo kan zargin badakalar dala biliyan shida a kwangilar tashar samar da hasken lantarki ta Mambila.



Wata babbar kotun birnin tarayyar Nijeriya, Abuja ta tasa keyar tsohon Ministan Ma'aikatar Lantarki na kasar, Olu Agunloye, gidan yarin Kuje don zaman wakafi bayan an gurfanar da shi a gabanta kan zargin badakala wajen bayar da kwangilar tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ke jihar Taraba.


An gurfanar da shi a gaban kotun Mai Shari'a J.O. Onwuegbuzie ne ranar Laraba kan tuhume-tuhume bakwai da ke da alaka da tafka almundahana wajen ba da kwangilar da kuma karbar sama da miliyan uku a matsayin na-goro.


Bayan an karanta tuhume-tuhumen ne tsohon ministan ya musanta zargin da aka yi masa yana mai cewa bai aikata laifi ba.


Sai lauya mai gabatar da kara, Abba Mohammed, ya nemi kotu ta tsayar da ranar da za a fara shari'a kuma ta tura tsohon ministan zaman wakafi.


Shi kuma lauyan wanda ake tuhuma, Adola Adedipe, ya sanar da kotun cewa shi ya riga gabatar da bukatar neman belinsa ya kuma nemi kotun ta ba da belinsa tare da ajiye tsohon ministan a hannun hukumar EFCC.


Sai dai Mai Sharia Onwuegbuzie ya sa a kai tsohon ministan gidan yarin Kuje zaman wakafi zuwa ranar 11 ga watan Janairu inda za a saurari bukatar neman belinsa.


A watan Disamba hukumar EFCC ta ayyana tsohon ministan a matsayin wanda take nema ruwa-a-jallo kan zargin badakalar dala biliyan shida a kwangilar tashar samar da hasken lantarki ta Mambila.


An dade ana rikici a kotu kan kwangilaR da aka fara bayarwa a shekarar 2003 lokacin mulkin tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo.

Post a Comment

0 Comments