Ana ci gaba da tafka mummunan yaƙin da aka fara tun wata tara da suka wuce, tsakanin janar ɗin soji biyu na Sudan

Ana ci gaba da tafka mummunan yaƙin da aka fara tun wata tara da suka wuce, tsakanin janar ɗin soji biyu na Sudan.



Hare-haren sama da ruwan bama-bamai da luguden wuta. Ƙarancin abinci da magunguna. Fiye da mutum 12,000 sun mutu. Ɗaruruwan mutane sun rasa muhallansu.


Ana ci gaba da tafka mummunan yaƙin da aka fara tun wata tara da suka wuce, tsakanin janar ɗin soji biyu na Sudan, lamarin da ya ta'azzara abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin rikicin da ya fi raba mutane da muhalkansu a duniya tare da tunkuɗa ƙasa ta uku mafi girma a Afirka a cikin masifa.


A cewar wani ɗan sa kai a wani ɗakin ba da agajin gaggawa a Bahri, wani birni da yake arewa da birnin Khartoum, kayan abincin da ke kantuna da wuraren ajiya a yankin suna ta ƙarewa.


Monzer O. mai sana'ar nazari kan harkokin kudade ne. Amma yakin basasar Sudan - wanda dakarun sojin kaar karkashin Abdel Fattah al Burhan (SAF) suke yakar mayakan RSF da Mohamed Hamdan Daglo ke wa jagoranci - ya janyo dakatar da wannan aiki da yake yi koyaushe.


A yanzu, matashin mai shekara 32 ya sadaukar da kansa ga wata cibiyar bayar da taimakon gaggawa, yana rarraba abinci ta hanyar "takkyah" ko dakin dafa miya malakar gwamnati, da ma wasu ayyukan alheri ga jama'ar yankin. a yayin da yaki ya hana shigar da kayan abinci a yankunan.


A yanzu ana sayar da kilo din tumatur daya kan Fan din Sudan 9,000, kusan dalar Amurka $13. Monzer ya kuma bayyana cewa rikicin na nufin ana takura wa mazauna yankunan da rikicin ya shafa diban ruwa daga kogin Nil don sha, wanko da girke-girke.


"Yanayin ya munana matuka, kuma ba za mu iya tunkarar wannan matsalar mu kadai ba," in ji Monzer. "Dole a samar da yankunan zaman lafiya ta yadda kungiyoyi za su samu damar unguwanni su bayar da taimakon gaggawa."

Post a Comment

0 Comments