ANA SHIRYE SHIRYEN YAƘI GABA DA GABA TSAKANIN HIZBULLAH DA ISRA'ILA

 ANA SHIRYE SHIRYEN YAƘI GABA DA GABA TSAKANIN HIZBULLAH DA ISRA'ILA.....



Rahotanni na fitowa daga Israila cewa Dakarun tsaron Israila na gudanar da wani gagarumin jigilar kayayyaki zuwa kan iyakar su da Lebanon.

Hizbullah ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta fiye da wata guda da ta gabata, kuma tana kai hari kan cibiyoyin soji a arewacin Isra'ila.

Har ila yau janyewar dakarun daga Gaza sannu a hankali wata alama ce da ke nuna cewa kashi na biyu na rikicin, wato; Za a fara yaƙi tsakanin Hizhullah da Israila.

A kwanakin nan, Amurka na kai wa Israila makamai masu tarin yawa, da suka hada da jiragen yakin F-16 da F-35.

Hezbollah tayi amfani da Makami mai linzami "Falaq-1" a karon farko wajen kai hari kan sansanin Israila.

Muhd Bala Afuwa

Post a Comment

0 Comments