CBN ya biya kusan dala biliyan 2 daga cikin bashin kudaden waje da ake binsa ''Cikin watanni ukun da suka gabata, CBN ya yi nasarar rage bashin kudaden da ake binsa, wanda ya kai kusan dala biliyan biyu,” a cewar mai magana da yawun Bankin, Hakama Sadi Ali a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.

 Babban Bankin Nijeriya CBN ya biya kusan dala biliyan biyu a matsayin bashin kudin kasashen waje a cikin watannin uku da suka gabata a wani mataki na rage yawan kudin da ake bin kasar.




Mai magana da yawun bankin ta bayyana cewa sai dai har yanzu karancin kudaden na ci gaba da haifar da mummunan tasiri ga kudin Naira na kasar.


Akwai akalla dala biliyan 7 na kudaden kasuwannin kasashen waje da suka makale a kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a Afirka, lamarin da ya sanya fargaba a zukatan masu zuba jari, sai dai CBN ya yi alkawarin biyan kudaden don bai wa kasuwar canjin kudi ta duniya kwarin gwiwa.


''Cikin watanni ukun da suka gabata, CBN ya yi nasarar rage bashin kudaden da ake binsa, wanda ya kai kusan dala biliyan biyu,” a cewar mai magana da yawun Bankin, Hakama Sadi Ali a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.


“Wannan yana jaddada irin kokarin da Bankin ke yi wajen magance matsalolin da suka kunno kai tare da inganta kasuwar canji.''


Nijeriya na fama da karancin kudaden kasashen waje saboda raguwar hako fetur, wanda shi ne abin da kasar ta fi fitarwa zuwa kasashen waje inda take samun kusan kashin 90 cikin 100 na dalar da ke shiga kasar.


A cewar Sadi Ali, a baya-bayan nan CBN ya biya dala miliyan 61.64 ga kamfanonin jiragen sama na kasashen waje, wadanda suka sayar da tikiti a farashin kudin kasar na Naira amma ba su samu damar fitar da kudadensu daga kasar ba.


Zuwa karshen watan Nuwamba kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suna bin sama da dala miliyan 700.


“Wadannan kudaden na nuni da irin kokarin da CBN ke yi na daidaita tare da rage duk wasu basussuka da ake bin kasar da nufin rage matsin lamba a kan farashin canji a kasar,” in ji Sadi Ali.


Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi alkawarin bunkasa kudaden kasashen waje da ke shigowa kasar ta hanyar jawo sabbin masu zuba jari, da habaka hako mai da kuma gyara kasuwar canji a Nijeriya.

Post a Comment

0 Comments