Dan jarida Umar Abdu ya bukaci gwamnati da ta gudanar da cikakken bincike a kan duk wani digirin da aka bayar a jamhuriyar Benin da Togo.

Dan jarida Umar Abdu ya bukaci gwamnati da ta  gudanar da cikakken bincike a kan duk wani digirin da aka bayar a jamhuriyar Benin da Togo.



Umar Audu, dan jarida a boye wanda ya yi nasarar samun digirin digirgir a jamhuriyar Benin, a cikin makonni shida, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki duk wani digirin da aka baiwa ‘yan Najeriya daga cibiyoyi na kasashen Benin da Togo. 

Gwamnatin kasar ta ce tana gudanar da bincike kan zargin karbar takardun digiri daga kasar Benin, sai dai ba ta ce komai ba game da dimbin digirin bogi da tuni ake yadawa a kasar. 

Har yanzu dai ba a bayyana a hukumance ba kan iyakar binciken da aka tsara zai kai da kuma yadda za ta yi hulda da jami’o’in da abin ya shafa a jamhuriyar Benin da Togo kan badakalar da dan jaridar Daily Nigerian da ya  boye ya bankado wanda har ya yi nasarar yin rijistar da youth Service Corp bayan samun digiri a cikin makonni shida. 

Wani farfesa a Jami’ar Legas, Victor Ariole, ya yi tsokaci a kan hukumcin gamayya na jami’o’in da ke yankin Afirka da kuma dubban daliban da ke karatu a cikinsu a halin yanzu.

Ariole ya ce a maimakon haka kamata ya yi gwamnati ta ware jami’o’i da daliban da suka yi kuskure. 

Dan jaridar da ke boye, Umar Audu, ya ce ya zama wajibi gwamnati ta gudanar da cikakken bincike a kan duk wani digirin da aka bayar a jamhuriyar Benin.

Post a Comment

0 Comments