Dan majalissar tarayya Yusuf Adamu Gagdi ya maida martani ga matar da tayi munanan zarge-zarge a kan matarsa Laylah Ali Uthman da ma sauran al'umma.

Dan majalissar tarayya Yusuf Adamu Gagdi ya maida martani ga matar da tayi munanan zarge-zarge a kan matarsa Laylah Ali Uthman da ma sauran al'umma.



A saƙon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito, Gagdi ya fara ne da cewa:


"Na gode da samun canjin suna. Domin zaman lafiyarta canjin suna ba wani abun ƙi bane. Amma duk da haka, ku tambayi asalin wadda ta ƙirƙiro sunan da ake faɗa cewa "Hauwa mai tuwo-tuwo", shin tana ina ? Za ta je ta maimaita kalamanta na ƙarya da ƙazafi da ta yi wa matata. Yanzu haka ba za ta iya yin kwana biyu a tsare ba, kuma ba za ta iya gabatar da hujjojin da ta ce tana da su ba". A cewarsa.


Gagdi ya cigaba da cewa "ku karanta abin da ke bakina, zan tabbatar da cewa ta je gidan gyaran hali batare da ta gabatar da bidiyo, hotuna da saƙonnin kartakwana da sautukan murya na matata da koma waye ba, ba ma wai iya wanda ta ambata ba". Bisa ga dukkan alamu tana so ta je gidan gyaran hali na Kuje ta cinye wasu ƴan shekaru tare da abokan harƙallarta". In ji shi.


Daga nan ya ƙara da cewa "Jama'a, ku faɗi duk abin da kuke son ku ce, zan kasance a bayan matata a kowane irin hali na farin ciki da baƙin ciki". A cewarsa.


Adamu ya ƙarƙare da cewa "Matana (Iyalina) ba su je ko'ina da kowa ba...".

Post a Comment

0 Comments