Dangote ya yi karin haske kan ziyarar da EFCC ta kai ofishinsa

 Dangote ya yi karin haske kan ziyarar da EFCC ta kai ofishinsa.




A wata sanarwa da kamfanin na Dangote ya fitar, ya ce ziyarar tana da nasaba da batun canjin kudin waje da Babban Bankin Nijeriya ya bai wa kamfanin tun daga shekarar 2014 zuwa yanzu.


Shugaban kamfanin Dangote Aliko Dangote ya yi karin haske kan wata ziyara ta baya-bayan nan da jami’an EFCC suka kai wa kamfaninsa.


A wata sanarwa da kamfanin na Dangote Group ya fitar, ya tabbatar da cewa jami’ai na EFCC sun kai musu ziyara sannan ya ce suna taimaka wa jami’an na EFCC wurin gudanar da bincike.


Jami’an na EFCC sun kai ziyara hedikwatar ta Dangote domin neman bayanai kan canjin kudaden kasashen waje da Babban Bankin Nijeriya ya bai wa kamfanin tun daga shekarar 2014 zuwa yanzu.


A sanarwar da kamfanin ya fitar, ya ce: “ A ranar 6 ga watan Disamba, mun samu takarda wadda take bukatar karin bayani game da canjin kudaden waje wanda Babban Bankin Nijeriya ya bai wa kamfaninmu tun daga 2014 zuwa yau. Mun gano cewa an tura irin wannan wasikar ga kamfanoni 51 inda ake neman irin wannan bayanin da kuma irin lokacin.


“EFCC ba ta nemi wani karin bayani ba kuma ba ta girmama bukatarmu ta kara mana lokaci ba inda ta bukaci lallai sai an ba ta cikakkun bayanai na wadannan lokutan. Duk da wannan takura, mun bai wa hukumar EFCC tabbacin mu na bayar da bayanan, kuma mun yi alkawarin bayar da takardun a rukuni bayan rukuni yayin da muke kammala tattara su.


“A ranar 4 ga watan Janairu, jami’anmu sun kai rukunin farko na wadannan takardu ga EFCC. Sai dai jami’an na EFCC ba su karbi wadannan takardun ba inda suka dage kan sai sun ziyarci ofishinmu domin karbar irin wadannan takardun kai tsaye.


“Yayin da wakilanmu ke ofishin EFCC domin kai takardun, sai jami’ansu suka tafi ofishinmu domin neman takardun a wani yanayi wanda aka yi domin kawo mana cin mutunci. Abin lura shi ne yadda jami’an ba su dauki wata takarda ko fayil daga babban ofishin mu ba a lokacin da suka kai ziyarar, kasancewar tuni aka kai musu ofishin su.


“Dole ne mu jaddada cewa, a saninmu, ba a tuhumi wani kamfani da ke cikin rukunin kamfanoninmu ba. A halin yanzu dai muna amsa bukatar neman bayanai ne kawai don taimaka wa EFCC kan binciken da suke yi,” in ji Dangote.

Post a Comment

0 Comments